Kwana Daya Da 'Yan Bindiga Suka Kashe Uwa An Samu Jariri Yana Barci Saman Banta

Kwana Daya Da 'Yan Bindiga Suka Kashe Uwa An Samu Jariri Yana Barci Saman Banta

An Samu Jaririn Yaro Raye Bisa Ban Mahaifiyarsa Kwana Daya Bayan 'Yan Bindiga Sun Harbe Mahaifiyarsa

Jaririn Yaro Dan wata bakwai da haihuwa da aka radawa suna Habibu an same shi a raye yana barci saman ban Mahaifiyarsa awa 24 bayan da 'yan Bindiga suka Harbe Mahaifiyarsa ta rasu nan take kan hanyar Pandogari-Allawa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Manema labarai sun samu labarin 'yan Bindigar sun tare hanyar ne a daren Sallah suka harbe fasinjoji shida ciki har da dalibar sikandare dake aji biyar a Makarantar Maryam Babangida a Mina Mai suna Hauwa Aliyu da mahaifiyar Jaririn da aka gani a goye  Kuma duka sun rasu.
Shugaban kungiyar matasa Lakpma Jibril Allawa ya ce Yaron Mai karama na cikin wadanda suka tsira in da aka kashe mutum shida.
Masu sintiri ne da suka tafi don kwaso gawar wadanda 'yan Bindigar suka kashe anan ne suka samu Yaron Yana barci saman ban Mahaifiyarsa da aka kashe, da take goye da shi.