Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da fara aikin tantance bayanan ma'aikatan ta domin fitar da sahihai dana bugi.
Wannan bayanin na ƙunshe ne a sanarwar da Jami'in Yaɗa Labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Murtala Gotomo ya fitar a Birnin Kebbi a yau Alhamis a birnin jiha.
Mukaddashin Shugaban Ma'aikata Safiyanu Garba Bena, ya umarci dukkan manyan sakatarorin jihar da su haɗa bayanan ma'aikatansu su kai masa ofishinsa da gaggawa ba tare da bata wani lokaci ba.
Bena ya ce hakan zai baiwa gwamnati dama ta san adadin ma'aikatan ta sannan ta samu damar cire bara-gurbi daga cikinsu don kara inganta aiki a jihar.
Ya ƙara da cewa aikin tantancewar zai baiwa gwamnati damar gane cewa biliyoyin Naira da ta ke kashewa wajen albashi na tafiya ne ga ma'aikata na kwarai ko kuma no bogi ne, in ya so sai ta riƙa samun rara na albashi.
Hakan nada matukar alfanu ganin yanda gwamnati ke kashe kudi amma sukan tafi ba in da ya kamata ba.
Tantancewar za ta baiwa gwamnati sanin yawan ma'aikatan da ke cikin tsarin biyan albashi a jihar da kuma irin walwalar da za ta samar musu.