Ana Dakon Ma'aikatun Da Tambuwal Zai Tura Sabbin Kwamishinoninsa

Ana Dakon Ma'aikatun Da Tambuwal Zai Tura Sabbin Kwamishinoninsa

Gwamnan Sakkwato  Aminu Waziri Tambuwal ya rantsar da Honarabul Dahiru Yusuf Yabo da Akibu Dalhatu a matsayin kwamishinoni mambobi a majalisar zartarwa ta jiha  a satin da ya gabata.
A wurin rantsuwar Tambuwal ya ce naɗin an yi shi ne kan cancanta ya bayyana tsammaninsa ga samun cigaban gwamnati ga gudunmuwar da za su bayar a jiha.
A lokacin da yake taya murna ga waɗanda aka baiwa muƙamin Tambuwal ya yi kira gare su da su yi amfani da basirarsu don samun nasarar nauyin da aka ɗaura musu.

Mutanen Sakkwato suna dakon wuraren da gwamna zai tura kwamishinonin da ya rantsar ganin kafin naɗa su ba a san wata ma'aikata da ba kwamishina ba kuma ba a samu bayanin an ƙirƙiri sabbi ba.

Managarciya ta yi ta karo da jita-jitar da ake yaɗawa a gari cewa wasu kwamishinoni ne biyu za su ajiye aiki hakan ya sa aka naɗa sabbin don maye gurbinsu, wannan maganar har yanzu ba ta tabbata ba.

Wasu na ganin gwamna zai ƙirƙiri wasu ma'aikatu ne da zai kai mutanen don ba da tasu gudunmuwa, ko yaya ne dai gwamnati za ta samar da wurin aiki gare su domin ba a kwamishina da bai da ma'aikatar da yake kula da ita, kamar yadda wasu masu taimakawa gwamna suke a jihar Sakkwato(S.A albashi ne kawai).