PDP Ta Ƙalubalanci Gwamnan Zamfara Kan Biliyan 31 Na Tsaro
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau.
Jamiyyar PDP a Jihar Zamfara, ta kalubalanci gwamna Bello Matawalle akan matsalar tsaro da ya amshi sama da naira biliyan 31 ,a cikin shekaru biyu da rabi da yayi na mulkin Jihar kuma kwaliya kwaliya taki biyan kudin sabulu.
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na jihar, Furofesa Kabir Jabaka ne ya bayyana haka alokacin da ya ke amsa tanbayoyin manaima labarai a Gusau.
Furofesa Jabaka ya bayyana cewa, gwamna Matawalle na watanda da kudin al'ummar Jihar Zamfara,ga wasu manyan Ma'aikatan gidan Gwamnati da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar da mataimakinsa da kuma sauran 'Yan majalisin kuwane wata akwai kasafi na musamman da suke samu daga lalitar Asusun Gwamnatin jihar wanda haka ya sabawa doka.inji Furofesa Jabaka.
Furofesa Jabaka kuma tabbatar da cewa,suna da aklaliman kudadan ake watanda da kudin Jihar na kowane ofishin da kuma yadda ake kasafta su.
Jamiyyar PDP ta kalubalanci gwamna Matawalle akan rashin Ko inkula da yake ma al'ummar Jihar ta Zamfara,dan abun bantakaici shine ana kashe mutane Amma Mai girma gwamna Matawalle na Kasar Nijar kalon kokuwa.inji Jabaka.
Kuma Jabaka ya kalubalanci gwamna Matawalle akan gazawar sa na kammala aiki koda daya ne wanda aka kammala aka kuma bude shi.
managarciya