Hasashen Malami A Sakkwato Kan Manir Dan'iya Ya Tabbata

Bayan watanni da kalaman malamin tsohon mataimakin Gwamnan Sakkwato wasu abubuwa sun faru da shi wanda mafi rinjayen mutane a jihar ke dangantawa da koma bayan tafiyar siyasarsa, abin da wasu masu nazari ke ganin hasashen malamin na iya tabbata.

Hasashen Malami A Sakkwato Kan Manir Dan'iya Ya Tabbata
 
Wani malamin addini a Sakkwato da ya yi hasashen tsohon mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya ba zai gaji tsohon  Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a zaben 2023 ya tabbata.
Malamin ya fitar da wani faifan bidiyo wanda Managarciya ta samu a watannin baya, in da kalaman nasa suka tayar da hazo a siyasar Sakkwato, wasu suka rika kallon malamin a matsayin wanda ya kauce hanya don bai hada sani da Allah ba, wanda ya san abin da kowa zai samu, wasu kuwa nada ra'ayin wannan ilmi ne da ake samu kan taurari.
Bayan watanni da kalaman malamin tsohon mataimakin Gwamnan Sakkwato wasu abubuwa sun faru da shi wanda mafi rinjayen mutane a jihar ke dangantawa da koma bayan tafiyar siyasarsa, abin da wasu masu nazari ke ganin hasashen malamin na iya tabbata.
A kwanannan malamin ya sake yin wata hira aka yada a kofofin sadarwar zamani in da ya sake jaddada hasashensa kan Manir Dan Iya, "Taurari sun canja wanda zai gaji Tambuwal yana cikin gwamnatinsa tare da shi, Maniru baya cikin  wadan da za su yi gwamna, cikin kwamishinoni ne zai gaji Tambuwal," a cewarsa. 
Sai dai anan hasashen nasa ya sha kure domin Gwamna Mai ci Dakta Ahmad Aliyu Sokoto baya cikin gwamnatin Tambuwal a lokacin da aka yi hasashen.