APC Ta Sanya Miliyan 20 Kudin  Fom Ga Mai  Neman Takarar Shugabancinta

APC Ta Sanya Miliyan 20 Kudin  Fom Ga Mai  Neman Takarar Shugabancinta

Shugaban jam'iya na kasa zai sayi fom na neman tsayawa takara kan miliyan 20 ga duk wanda yake bukata.

Mataimakin Ciyaman zai sayi fom dinsa kan miliyan 10, sai sauran kujeru a majalisar zartarwa kan miliyan biyar kowanensu.
Taron zabar shugabanin kasa za a yi shi ne 26 ga watan Maris.
Sayar da fom na neman tsayawa takarar an soma shi ne a ranar Litinin za a rufe a ranar Jumu'a ta wannan satin. 

Jam'iyar ta bar mutane cikin rudu da rashin sanin makama domin matsayar da take rayawa an samar wasu na ganin da gyara, har yanzu ba a samu matsaya kwakkwara ba.