Rikicin APCn Sokoto Ministan shari’a ya ayyana Mainasara a matsayin halastaccen shugaba.
Sam mu bamu san da zancen ba cewar APC Bangaren Sanata Wamakko.
Daga Aminu Alhussaini Amanawa, Sokoto.
Babban lauyan gwamnatin tarayya kana ministan tsaro na kasa Abubakar Malami ya ayyana sunan Mainasara Sani a matsayin zababben shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto.
Kalaman ministan dai na zuwa ne a wajen gabatar da manyan bakin da suka halarci bikin rabon kayan tallafi da dan majalissar wakilai na jihar mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Abdullahi Balarabe Salame yayi.
A cewar ministan Mainasara Sani na bangaren Sanata Gada ne halastaccen shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto.
pan style="font-size: large;">“Zababben shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto, tabbatacen shugaba wanda shari’a ta tabbatar Alhaji Mainasara Sani inji ministan Abubakar Malami”
Bangaren Sanata Abubakar Gada ne dai suka bayyana zaben Mainasara Sani wanda ministan ya tabbatar da sahihancin zaben nasa, yayin dayan bangaren na sanata Wamakkon ya zabi Isa Sadiq Achida a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto a zabukkan shuwagabannin jam’iyyar daya gabata a baya.
Wannan dai na zuwa ne sa’ilin da jam’iyyar APC a jihar Sokoto ke fama da rikicin shugabanci, abinda ma ya sanya uwar jam’iyyar ta kasa kasa mika takardar jagorancin jam’iyyar ga zababben shugaban ta na jihar Saboda rikicin na shugabanci tsakanin bangaren Sanata Wamakko da kuma na Sanata Abdullahi Gada.
Sai dai a taron manema labarai da bangaren Sanata Wamakko ya gudanar dai, shugaban jam’iyyar bangaren Wamakko Isa Sadiq Achida, ya bayyana cewa su basu masan da zancen ba, hasalima ministan ya sauka daga mukamin sa a cewar Isa.
“Kasancewar sa babban lauya, masani shari’a sam bai kyautu yazo yana goyon bayan wani bangare ba, kan rikicin APC na Sokoto domin lamarin na a gaban Kotu, kuma wannan kasawace wajen gudanar da aikin dake kansa yake mayar da hankali wajen rura wutar rikicin shugabancin jam’iyyar APC jihar Sokoto.
Acewar Isa Sadiq Achida abin Allah waddai ne ace ministan shari’aya bayyana sunan Mainasara Sani a matsayin halastaccen zababben shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto.
“Kasantuwar lamarin na a gaban kotu, to inaga sam bai kyautu ba, ace Abubakar Malami ya ayyana sunan wani a matsayin halastaccen shugaba, tunda dai Malami ba shine shugaban jam’iyyar na kasa ba, ko kuma yake rike da wani mukami a jam’iyyar, kuma bisa wannan ne ma nake kira ga uwar jam’iyya ta kasa dasu sanya ido kan Malami domin yana da wata alaka da gwamnatin PDP mai jagorancin jihar Sokoto inji shi”.
Suma dai mambobin Majalisar Dokokina jiha na Jam'iyyar APC 13 a sakkwaton, sun yi tir da Allah wadai da kalaman Ministan da Sanata Ibrahim shekarau da suka yi a wajen rabon kayan tallafi da suka halarta da Abdullahi Balarabe Salame yayi, na ayyana sunan Mainasara Sani a matsayin shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Sokoto.
'Yan Majalisar sun dai bayanna hakan ne, suma a wani taron manema labarai da suka gudanar da jagoran Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto Hon. Bello Isah Ambarura ya jagorata.
Acewar su, sam bai kamata ba ga irin Minista Malami ya furta wadannan kalaman a matsayin sa na babban lauyan gwamnatin tarayya.
“Wannan maganar tana a gaban kotun daukaka kara, to bai Kamata wani mai matsayi irin na malami ya riga malam masallaci ba, ya ce hakan zai sanya shakku ga jama'a ga wani hukunci indai har ministan shari'a na shiga gaban kotun.
Bisa wannan ne sukayi kira ga reshi da Sanata Ibrahim shekarau da su koma jihohin su domin fuskantar matsalolin da suke fama da su a cikin Jam'iyyar su, kafin ruruta wutar a sauran jihohi.
Bello Isah Ambarura ya kara da jaddada goyon bayan Yan Majalisar su Goma sha uku ga jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin Jagoran Jam'iyyar APC na Jihar Sokoto.
Haka kuma sun bayyana goyon bayan su ga shugabancin Isah Sadiq Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar Sokoto.
Rikicin shugabanci a jam’iyyu dai ba sabon lamari bane a najeriya a cewar Dr Ibrahim Baba Sha Tambaya malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa dake jami’ar Usmanu Danfodito ta sakkwato.
“A yanda jam’iyyun siyasar Najeriya ke tafiyar da lamurran su, ba sabon lamari bane, kuma muna tunanin nan gaba zai kai su ga wani matsayi”
Wannan dai na zuwa ne sa’ilin da zabukkan 2023 ke dada karasowa, lamarin da jam’iyyun siyasa suka daura damarar in bakayi bani wuri.