NDLEA ta kama tsohon ɗan ƙwallon ƙafa kan safarar hodar ibilis

NDLEA ta kama tsohon ɗan ƙwallon ƙafa kan safarar hodar ibilis

Hukumar NDLEA ta kama wani tsohon dan ƙwallon kafa, Emmanuel Okafor a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja, bisa laifin safarar hodar iblis.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi a Abuja, inda ya ce an kama Okafor ne a lokacin da ya taso daga Sao Paulo, Brazil ta birnin Addis Ababa.

Ya tashi ne a cikin jirgin Ethiopian Airlines.

Babafemi ya bayyana cewa wanda ake zargin yana ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.4 da aka boye a hannun jakunkunansa da kuma a saman jakunkunan.

Ya kara da cewa an kama matashin mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia ne a ranar 26 ga watan Satumba, bayan jami’an yaki da muggan kwayoyi sun bankado inda ya boye haramatattun kayan .

“A yayin binciken farko, Okafor ya ce shi dan kwallon kafa ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya, Enugu FC, inda ya yi wasa har tsawon shekaru hudu kafin ya tafi Sri Lanka a shekarar 2014.

"Ya ce ya koma Brazil daga Sri Lanka bayan ya yi wasa na kaka biyu, amma bai iya ci gaba da buga kwallon kafa a Brazil ba saboda ba shi da takardu," in ji Babafemi