Tambuwal ya yi kalamai masu ratsa zuciya kan Shugaaba 'Yar'aduwa

Tambuwal ya yi kalamai masu ratsa zuciya kan Shugaaba 'Yar'aduwa
 

A ranar 5 ga watan Mayun 2010, Allah ya karbi rayuwar shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, bayan fama da rashin lafiya. 

A rayuwa, wasu lokuta kan zamo abin tunawa, yayin da wasu lokutan kan zamo tarihi wanda ba zai mantu ba, a cewar Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
Tambuwal, a shafinsa na Twitter, ya ce ranar 5 ga Mayu, 2010 ta kasance abar tunawa ga Nijeriya da al’ummarta, kuma ta shiga tarihi na har abada.
A irin wannan ranar, shekaru 14 da suka gabata, mai kishin dimokradiyya kuma shugaba na gari, Mai Girma Umaru Musa 'Yar'aduwa GCFR, mutun mai tawali'u, hangen nesa, manufa mai kyau, ya shaki numfashinsa na karshe. "Wannan rana mai cike da juyayi ta sauya yanayin siyasar kasarmu, ta bar wani gibi da zai yi matukar wahalar cikawa." 
"Yar'aduwa ya kasance mai kishin kasa wanda ya yi imani da samar da tsarin dimokuradiyya mai kyau, kuma ya dukufa wajen samar da hadin kan Najeriya.
"Ya kasance jigon siyasa a gare ni da wasu da yawa waɗanda suka yi imani da gina cibiyoyi da tsare-tsare masu ƙarfi maimakon dogaro ga wasu mutane 'yan kalilan masu ƙarfin fada aji." 
Tsohon gwammnan ya shiga sahun 'yan Najeriya wajen mika sakon ta'aziyya, alhini da kuma tunawa da "wannan hazikin mutum mai yakana da hangen nesa."