Bayan Kai Hari A Gidan Yari An Kama Fursunoni 7 Da Suka Tsere A Jos

Bayan Kai Hari A Gidan Yari An Kama Fursunoni 7 Da Suka Tsere A Jos

An cafke hursunoni  7 da su ka tsere bayan da 'yan bindiga su ka kai hari a gidan gyaran hali na Jos, Jihar Filato.

 

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an  ne a wani shingen bincike na jami'an tsaro da a ka girke a cikin garin Jos.

 
Jaridar ta rawaito cewa ɗan hursunan guda ɗaya kuma da ya tsere ya kai kansa ga jami'an 'yan sanda.
 
Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa an ritsa 'yan bindiga a cikin gidan yarin bayan da su ka yi yunƙurin ɓalle shi. 
 
'Yan bindigan, ɗauke da muggan makamai ne su ka kai hari gidan gyaran halin a Jos.
 
Francis Enobore, kakakin gidan gyaran halin ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
 
Ya ce 'yan bindigan sun dira a ƙofar shiga gidan gyaran halin ne da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, inda su ka nufi babbar ƙofar shiga.
 
Su na dosar ƙofar, in ji Enobore, sai su ka buɗewa ma'aikatan gurin wuta, su ma kuma su ka maida martani, inda a hakan ne maharan su ka samu damar ɓalle ƙofar su ka shiga harabar gidan.
 
Bayan sun samu shiga cikin gidan, ai kuwa sai a ka ritsa su bayan da a ka gayyato sauran jami'an tsaro su ka yi wa gidan gyaran halin ƙawanya, in ji Enobore.
 
Enobore ya ƙara da cewa an kuma ƙaro dakaru da ga shalkwatar gidajen gyaran hali.
 
Ya ƙara da cewa yanzu dai an shawo kan lamarin, bayan da gamaiyar jami'an tsaro da a ka girke a wajen su ka mamaye gidan gyaran halin kuma sun fi ƙarfin maharan.
 
Yayin da ƴan bindigar su ka shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, Enobore ya sanar da cewa za a ci gaba da bada bayanai da zarar an wasu wani ci gaba a bisa lamarin.
Matsalar tsaro a Nijeriya kullum kamari take yi da zaran an kulle nan sai can ya balle.
Akwai bukatar jami'an tsaro da gwamnatin Nijeriya su sauya sallon yanda suke gudanar da aiyukka kawar da batagarin kasa.