Abin Da Ya Yi Sanadin Rasuwar Gwamnan jihar Ondo 

Abin Da Ya Yi Sanadin Rasuwar Gwamnan jihar Ondo 

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya na ba da rahotannin cewa Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.

Ya rasu yana da shekara 67, bayan a cewar rahotanni, ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da kansar mafitsara.

Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan Gwamna Akeredolu ya rubuta wasikar tafiya neman lafiya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Sama da wata biyu bayan dawowar Gwamna Rotimi Akeredolu daga tafiyar jinyarsa ta farko, ba a gan shi a bainar jama'a ba.

A watan Yuni ne gwamnan ya karɓi hutun jinya na tsawon kwana 21, inda ya garzaya zuwa Jamus, sai dai ya gaza komawa gida a lokacin da hutun jinyar nasa ya ƙare.

Lokacin da Rotimi Akeredolu ya koma Ondo daga bisani kuma, sai ya aika wa majalisar dokokin jihar inda ya sake neman ƙarin hutun jinya a ranar 15 ga watan Yuli.

An zaɓi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa'adi na biyu a shekara ta 2020.

Ɗan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya fara cin zaɓen gwamna a watan Nuwamban 2016.