Nasarar zaɓen Osun ya isa APC ishara a Gombe--Hajiya Uwani Hamsal

Nasarar zaɓen Osun ya isa APC ishara a Gombe--Hajiya Uwani Hamsal

Daga Habu Rabeel, Gombe.

Hajiya Uwani Usman, da ake kira Uwani Hamsal, tace nasarar zaben gwamnan jihar Osun da PDP tayi ya isa APC darasi a Najeriya musamman a jihar Gombe.

Tace jam'iyyar PDP ta shirya tsaf dan tunkarar babban zaben shekarar 2023 wanda idan Allah ya yarda za ta lashe dukkan kujerun ta wanda alama ta nuna hakan kuma Dan Barde zai zama gwamna da yardar Allah.

Hajiya Uwani, ita ce shugabar Mata ta karamar hukumar Gombe a tafiyar gidan Dan takarar gwamna Muhammad Jibrin Dan Barde, kuma tace shakka babu jam'iyyar za ta karbe mulki daga hannun yan koyo dama aro aka basu kuma sun kasa iyawa dan haka za su karbe mulkin su.

A cewar ta tana da tabbacin idan Dan Barde yaci zabe zai rungumi kowa da kowa a tafi tare dan shi bukatar sa shi ne a ceto jihar daga halaka  a hannun mutanen da basu iya ba kuma basa jin shawara.

Hajiya Uwani, ta ce gwamnatin APC ta shekara uku a karagar mulki amma basu da wani abu da za su nunawa mutane da za su yi kamfen da shi sai yunwa da fatara.

" Dan Barde shugaba ne abun kwatanta misali da shi wanda idan yaci zabe kowa zai shaida domin a yanzu ma da shi ba gwamna ba yana yin iya kokarin sa wajen yin adalci" inji ta.


Daga nan sai Uwani ta kara da cewa yadda mutane ke kara fita daga APC shi ne yake sa su kwarin guiwa kuma zaben jihar Osun ya zama zakaran gwajin dafi na cin dukka zabukan dake tafe a 2023, lokacin da Dan Barde zai kada dan takarar APC ya dauki kujerar.