HAƊIN ALLAH
Page 3
Har zuwa yanzu zuciyata bata amince na bayyana ma mahaifiyata cin amanar da mijina da ƙawata suka taru suka aikata min ba, amma na kasa sanin abin da zan ce mata, saboda abin ne ya zo abaza, kuma ban saba yi ma mahaifiyata ƙarya ba, amma sai na samu bakina da furta, "Ban da lafiya tun safe cikina ke ciwo Mama na rasa yadda zan yi." Wuf tai ta miƙe tana cewa, "Ba shakka haihuwar ce sai ki yi shiru to ki kama kuka? Ai ba a ɓoye irin wannan ciwon kamar yadda ba a yi ma shi kuka." Hijabinta ta ɗauka ta fice da uban sauri ina kallon sadda tai tuntuɓe da tudunkar ƙofar ɗakin amma ko a jikinta. Ba a jima ba sai naji sallamar Yayar mahaifiyata hakan yasa na fahimci zuwa tai ta kira min Yayarta tunda nice yarinyarta ta farko, tana jin kunya ta da nuna min kawaici ko da yaushe. Cikin ƙanƙanin lokaci akai ta bankamin rubutu da magunguna wai na sauƙin nakuɗa ne, ba yanda zan haka na jure naita amsa ina banka ma cikina sai dai ba a jimawa nake amayar da duk abin da na sha, sai kuma Yayar mahaifiyata tace wai fayar baka nake yi. Ban san dai me take nufi ba da abin da ta kira fayar baka ba, don haka da naga an takuramin nace mata "Ba fa yanzu Likita yace zan haihu ba juyawar kan yaro ce yace." Tace "Ko da naji, ai rubutun gidan Malam da aka amso indai haihuwa ce ana sha nan take ɗa ke faɗowa, to Allah Ya baki lafiya, nakuɗar tsaitsaye kike yi dai kenan." Ta ɗauki hijabinta ta fice da yake ba nisa da gidanta sai ga Mamana ta shigo ta dinga jera min sannu ta ɗauki mafeci tana min fiffita. Cikin ikon Allah wani barci ya sace a hakan. Na jima ina barci don sai yamma liƙis na tashi, na samu nayi sallar la'asar na ce ma Mama zan tafi tace, "Yau ba shi zai zo ɗaukar ki ba ne? Nasan abin da yasa tace hakan. Lokuta da dama mijina ke kawoni gidan yace na wuni zai zo mu tafi tare, shike nan ba zai zo ba sai dare har ƙarfe goman dare ina kaiwa ina jiran shi, tun abin bai damun Mamana har dai ta kai ga yi ma shi magana watarana, "Ni kam nace ina son in ce baka yarinyar nan ta dinga zama ɗakinta ba amfanin yawo nan ko dan saboda gaba." Ya yi murmushi yace mata, "Ai indai zata fita ta aje min makullin gida ban da damuwa da yawonta Mama, ita karin kanta ma bata taɓa nuna min zata fita ba, ni ne ke sata dole tana fitar kuma daga nan gidan sai gidanmu take zuwa ai." Mamana ta girgiza kai da yake mace ce da bata fiye magana ba balle shi da yake mazaunin surukinta na ɗiyarta ta farko don haka bata ce ƙala ba. Na tashi a hankali na ce na tafi jikina sanyi ƙalau ba alamar fara'a ko walwala balle annuri a kan fuskata balle a same shi a cikin zuciyata. Har zaure ta rakani tana gayamin idan dai naji abin bai bari na mu je asibiti na bita da to kawai.
Lokacin da na koma unguwarmu sai naga gungun mata ba shakka jikina ya bani gulmata suke, amma ya zan yi ? Naka shi ne ke bada kai. Na yi masu sallama na raɓa su zan wuce wadda tafi kowa surutu tace min "Amarya baki lafiya ne na ganki duk kin koɗe kin jeme?" Ɗaga mata kai nayi kurum na shige ta gabansu na wuce, amma sai jinta nayi tace, "Don Allah ki samu kwalli ki shafama idanunki duk sun koze kin yi wata hajaran-majaram dake abinka da farar mace bata kyan gani a damuwa." Ni kam ƙala ban sake cewa ba, na buɗe gidana na shige na maido ƙofar na rufe na tsugunna a gun na saki kuka mai ciwo.
Shiru-shiru ba labarin Deeni har akai magariba akai ishsha'i ba alamar Deeni, ni kam zuwa lokacin zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ni na kwanta falo kan kujera ina tilawar abin da na gani ya faru a cikin falon da idanuna. "Salamu alaikum." Sallamar magajiyar mijina ce nayi Babbar Yaya, da ƙyar na amsa sallamar ban tunanin ta isa ta ji amsawar da nayi mata duk kuwa jin da take taƙamar tana yi na magana ko da raɗa ce. Cikin sauri ta danno ɗakin tana jera min sannu kamar wadda na aika mawa nace ta taho ban lafiya. "Za ki iya daurewa mu je can gidanmu dake Jiddah?" Ɗaga mata kai nayi, domin yanzu ban da ikon buɗe ko bakina a yanayin da nake ciki ni kaina ina jin yadda zafin jikina ya mamaye inda na tashi. Hijabina kawai na saka muka fice ina taka ƙasa tana wani irin ƙara dimm-dimmm kaina na sarawa kamar zai fashe. A haka na samu muka isa gidansu tana jera min sannu ba iyaka.
A gidansu na iske Gaje sai da gabana ya faɗi haka kawai na ji damuwar tawa ta koma biyu, ban san kowa yasan da wannan maganar domin zubar da kimata ne da tashi shi kanshi mijin nawa. Ban san me ya faru ba naga dai wata Malamar asibiti ta shigo ance na gyara zata dubani, nai ta tunanin dubawar me za tai min amma dai ban tanka ba, bayan ta duba ni ne tace masu ba haihuwa bace ba. Ɗakin kishiyar Mamarsu Deeni aka ce mu kwana ni da Gaje, tana kwance ina zaune na yi tagumi ina tunanin abin da ya zame min jiki a ranar yau naji muryar Gaje na cewa, "Lallai Jiddah, Deeni ɗan rainin hankali ne, mun zo ni da Habib ya kawoni na kwana zai yi tafiyar kwana ya zo yace "A je a taho dake shi ya tafi gun aiki Katsina, kuma yaga kamar haihuwa za ki yi." Zuwa yanzu duk abin da za a ce Deeni ya yi bai ban mamaki tabbas zai aikata komai tunda har ya iya yin mirsisi ya ci amanata, don haka nayi shiru ban ce mata ƙala ba illa sabon kukan daya ƙwace min kawai, wanda Gajen itama ta tayani mu kai ta kuka tamkar an yi mana rasuwa, ita dai data gaji tai barci ta barni zaune ina tunanin rayuwar aurena hakan yasa kai tsaye na kwana zaune ina saƙawa da kwancewa amma daga ƙarshe na amince da shawarar ƙarshe da zuciyata ta ban, don haka asuba nayi na yi sallah na gama addu'a na tashi ban bi ta kan kowa ba na fice daga gidan ban zame ko'ina ba sai gidan auren ƙawata Safiya da yake ba nisa da gidan surukaina, sai dai ina zuwa ban iske ta ba sai mijinta yace min bata kwana gidan ba gidan Mamarta ta kwana, duk da na lura da kallon mamaki da tuhuma da yake bina da shi ban damu ba na juya kai tsaye na nufi gidansu Safiya.
Ina shiga na iske Mamarta a zaune ta yi tagumi nayi sallama ta amsa ta miƙe cike da mamaki ta jero min tambayoyin, "Jiddah lafiya kike tafe da farar safiyar nan? Me ke faruwa ne haka Jiddah? Kin ga yadda kika koma kuwa Jiddah ko dai baki lafiya ne?" Na samu da ƙyar na maida hawayen idona nace "Safiya na nan kuwa Mama?" Tace "Tun jiya da rana ta zo gidan nan a ruɗe da taji motsi sai ta zabura Allah Yasa dai lafiya don nayi-nayi ta gayamin damuwarta ta ƙi." Ni dai bance komai ba na nufi ɗakin da Safiya take ciki. Ina shiga ta zabura kamar zata riƙe ni ta kuma koma ta zauna tai shiru. Cike da tausan kaina na dube ta nace, "Safiya tsakanina dake duk wanda ya cuci wani Allah Ya saka ma shi, ban taɓa tunanin za ki iya aikata min abin da kika aikata ba, amma na barki da Allah shi ne zai saka mun idan har ina da haƙƙi a kanki to ba shakka nasan zai fitar mun da shi. A zama na dake nasan da zuciya guda nake tare da ke amma ba zan iya kwatanta da zuciyoyi nawa ke kike tare da ni ba... "Wai me ke faruwa ne Jiddah?" Cewar Mamarsu. Na girgiza kai nace "Ga ta nan ai Mama ta gaya maki abin da akai jiya." Amma Safiya tai mirsisi ta ƙi magana. Ganin Mamarsu ta dage sai ta ji abin da akai na gaya mata komai. Ban ankara ba haka ban zata ba kawai ji nayi muryar Mamar Safiya cikin kuka tana cewa, "ALLAH Ya tsine maki Safiya! Kin yi asarar rayuwarki, ko za ki yi irin wannan lalacewar bai kamata ki yi da mijin Jiddah ba, yarinya ƴar mutunci mai cike da karamci da tausayi kika aikata ma wannan mugun abin? Anya Safiya za ki gama lafiya kuwa? Ita dai Safiya bata tanka ba, sai ma nice da naga kukan Mamar ya yi yawa na dinga bata haƙuri ina goge nawa hawayen. Har ƙofar gida Mama ta biyo ni tana ban haƙuri na tafi zuciyata cike da tunani kala-kala, har na koma ba wanda yasan na fita a gidan na kwanta kan gado ina tuna asalin wacece ni, da ƙaddarar data saka na auri Deeni bayan ko a mafarkina ba shi ne ba.
A hankali faifan rayuwata ya soma juyawa tun daga lokacin dana tsinci kaina gaban Kakata da ƙullin kayana da mahaifiyata ta aje ta juya tai tafiyarta ko waige na bata yi ba.
Asalina * * *
Hauwa'u shi ne asalin sunana amma kasancewar babban suna ne dana ci na babbar gidansu mahaifiyata yasa ake kirana da Jiddah. Mahaifina Alh. Bishir (Dawa) ya auri mahaifiyata tun yana gaɓar ƙuruciyar gaske domin ya tsallake Yayyensa uku ringis ya yi aure su ba su yi ba. Kowa da Dawa kawai yake kiran mahaifina idan aka fita waje domin mutum ne mai son harkar shiga daji ya yi rayuwa, yafi son rayuwar dazuzzuka fiye data cikin gari. Suna zaune a garin Jalingo cikin gari, gidansu babu nisa sosai dana iyayensa amma tsabar abin a jininsa yake haka yake tsallake matarsa Salma ya ja zugar yaransa su wuce daji farauta daga can ya ɗebo magunguna na gargajiya kala-kala, da farko zamansu gwanin sha'awa amma daga baya sai yawon mahaifina ya takura rayuwar auren Mamata, hakan yasa suka dinga samun matsala wanda ƙarshe dai akace ta dawo cikin gidansu da zama ko da ya tafi kaɗaici ba zai dameta sosai ba. A haka aka haife ni da daɗi ba daɗi har aka yaye ni, tana da shigar wani cikin ne ya yi tafiyarsa daji inda ita kuma ta rantse bata zama ta gaji, ta ɗauki kayana ta wanke fes suka bushe ta ƙulle a kallabi ta kama hanuna bayan sallar la'asar ta kaini gaban Kakata tana zaune tana sallah ta juya ta fice. Daga nan ƙalubalen rayuwata ya fara.
Ku biyo Haupha dan jin wane ƙalubale ne wannan?
Taku a kullum Haupha