Da Kudin Noma Ne Na Samu Kudin Kamfena  a 2023---Bashir Gorau

Da Kudin Noma Ne Na Samu Kudin Kamfena  a 2023---Bashir Gorau

 

Matashi mai shekara 33 a duniya, Bashir Usman Gorau, wanda ya lashe zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya na mazaɓar Gada-Goronyo, ya bayyana inda ya samu kuɗin kamfen ɗin sa. 

Jaridar Daily Trust tace Bashir ya bayyana cewa ya samu kuɗin kamfen ɗin sa ne ta hanyar kuɗin da yake samu a noman da yake taɓawa. 
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da Gorau a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri'u 29,679, inda ya hana tazarce karo na biyar na Musa Adar na jam'iyyar APC, wanda ya 25,549, cewar rahoton The Cable.
A wata tattaunawa da gidan talbijin na Trust tv a shirin su na 'Daily Politics' ranar Talata, Gorau ya yi bayanin cewa da shi da maigidan sa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ba su taɓa amfani da kuɗin asusun jihar ba wajen yaƙin neman zaɓen su. 
"Kamar ni, na samu kuɗin kamfen ɗi na ne ta hanyar noma da kasuwancin da na ke yi. Kowa ya san cewa ni manomi ne, tambayi duk wanda za ka tambaya, a tsawon wata 14 da na yi bana riƙe da ofis." 
Gorau tsohon kwamishinan ci gaban matasa da wasanni ne na jihar Sokoto, ya yi takara a ƙarƙashin inuwar Peoples Democratic Party (PDP). 
Nasarar da ya samu ta ƙara yawan matasan da suka lashe kujerun ƴan majalisa a babban zaɓen 2023.