Muna Son Lashe Zaben Jihohi 25 a Zaben 2023----Shugaban PDP

Muna Son Lashe Zaben Jihohi 25 a Zaben 2023----Shugaban PDP


 Shugaban Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyanawa 'yayan jam'iyya cewa suna da tabbacin lashe zabe a jihohi 25 a zaben 2023. 
Ayu yace a 2023, PDP zata dawo da mulkin jihohi da yawa kamar yadda ta saba zamanin Obasanjo da Jonathan. 
Ya bayyana hakan ne bayan ganawar shugabannin jam'iyyar da yan takara kujerun gwamna ranar Laraba a hedkwatar jam'iyyar dake Abuja, rahoton Punch. 
A cewar Ayu, yan takaran sun gana da mambobin kwamitin don jin abubuwan da suke yi don nasara a zabe a jihohinsu. 
"Muna son nasara a jihohi 25 kamar yadda muka saba." 
"Muna son nasara a tarayya, a jihohi, majalisar dokoki da kujerun gwamna."