Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Al’ummar Hausawa da Fulani a Yobe ta Kudu sun sha alwashin bai wa Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni cikakken goyon baya a zaben 2023 mai zuwa, tare da bayar da tabbacin kada kuri’unsu ga yan takarar jam’iyyar APC, daga Shugaban kasa, gwamnan jihar da daukacin yan takarar jam’iyyar APC.
Da yake jawabi a wajen taron, dan majalisar dokokin jihar Yobe mai wakiltar mazabar Jajere, Ciroma Buba Mashio, a garin Ngelzarma dake karamar hukumar Fune, da yammacin ranar Jummu'a ya bayyana gagarumin taron a matsayin na hadin gwiwa tsakanin kungiyar Fulani makiyaya da Hausa dake Yobe ta kudu su ka shirya.
Ya ce gwamnatin Hon. Mai Mala Buni ta yi wa al’ummar yankin goma ta arziki wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da bunkasa yankin, tare da bai wa fitattun ya'yan yankin mukamai, samar da wuraren kiwo, gina makarantu dom makiyaya da sauransu.
“Saboda haka muna da dalilai da yawan gaske na zaben Sanata Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa, da sake zabar Gwamna Buni tare da sauran yan takarar APC a zabe mai zuwa."
A nasa bangaren, shugaban kungiyar Miyetti Allah na Nijeriya, Baba Usman Ngelzarma ya bayyana farin cikinsa bisa yadda dubban jama’ar da suka fito domin halartar taron hadin kan da aka yi domin karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.
“Fulanin jihar Yobe suna matukar alfahari da shugabancin ka, tare da cikakken goyon baya da kake ba mu. Wanda hakan ya zama wajibi mu gode maka. Kuma tarihin Masarautar Ngelzarma ba zai cika ba har sai an ambaci irin gudunmawar da ka bayar, musamman gina babban masallacin Jummu'a a wannan Fadar. Uwa-uba kuma tsayin daka da kayi waken ganin mun samu nasara a matsayin shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa.”
Har wala yau, shugaban Miyetti Allah ya yi kira da Fulani a yankin da cewa, “Dukaninmu a wannan yankin muna sane da goyon bayan da wannan gwamnati take bamu, wanda bisa ga haka za mu ci gaba da kasancewa masu biyayya ga gwamnati don ci gaban jama’armu. Saboda haka mu fito kwanmu da kwarkwata mu zabi jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.” in ji shi.
A jawabinsa ga mahalarta taron, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana gangamin a matsayin wata alama ta zaman lafiya da aka samu a jihar Yobe, sakamakon kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari da tsayuwar jami’an tsaro a karkashin gwamnatin APC. Ya ce ci gaban da ya hada Arewa maso Gabas baki daya. Ya ce, "Idan kun lura babu wanda aka caje kafin shigowa wannan babban taro; sabanin shekarun baya, mun gode wa Allah da ya ba mu zaman lafiya."
Buni ya bayyana cewa gwamnatin sa ta aiwatar da ayyuka da dama a kowace daya daga cikin mazabu 178 da ke jihar Yobe. Ya ce, “Mun gina tituna domin saukaka ayyukan tsaro a jihar, muna kokarin kammala aikin filin jirgin sama wanda wata rana za a yi amfani da shi wajen jigilar mahajjatanmu zuwa Saudi Arabiya da sauran harkokin yau da kullum.”
A karshe ya yabawa al’ummar Hausa/Fulani bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa inda kuma ya bukaci kungiyar Miyetti Allah da ta kara kaimi wajen kawo karshen rikicin makiyaya da manoma. Har wala yau kuma Gwamna Buni yaba da gudunmawar Sarakunan Gargajiya a jihar ke bayarwa ta fannin wayar da kan jama'a bisa dukkan manufofi da tsare-tsaren gwamnati.