Tinubu na son a a gudanar da sahihin zaɓe a 2027 – Abbas
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na son a gudanar da zaben 2027 cikin gaskiya da adalci fiye da na 2023.
Abbas ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karɓi tawagar Tarayyar Turai (EU), inda ya ce ana gyara Dokar Zabe ta 2022 domin tabbatar da sahihanci da ingantaccen tsarin zabe.
Ya ce an yi la’akari da matsalolin da masu sa ido na kasa da kasa suka bayyana a zaben 2023 a cikin gyaran dokar da ake yi.
Abbas ya kuma bayyana cewa majalisar dattawa da ta wakilai sun cimma matsaya kan ware batutuwan zabe a matsayin abu guda domin hanzarta gyaran, sannan a tura shi zuwa majalisun dokokin jihohi kafin karshen shekarar 2025.
Ya kara da cewa shawarwarin gyaran kundin tsarin mulki sun haɗa da ƙara kujeru na musamman ga mata da masu bukata ta mussaman da ba wa sarakunan gargajiya matsayi da ’yancin kuɗi, da gudanar da zabe a rana guda domin rage wahala da ƙarfafa fitowar masu kada kuri’a.
Ya roki EU da ta taimaka wajen yadawa da kuma wayar da kan jama’a game da gyaran, tare da jaddada cewa majalisar za ta samar wa INEC dukkan kayan aikin da ake bukata don inganta zaben 2027.
Shugaban tawagar EU, Barry Andrews, ya yaba wa ƙoƙarin majalisar wajen ƙarfafa dimokuradiyya a Najeriya.
managarciya