Mun haɗa kai domin yaƙar rashin tsaro----Gwamnonin Arewa maso yamma

Mun haɗa kai domin yaƙar rashin tsaro----Gwamnonin Arewa maso yamma

Gwamnonin Arewa maso yamma su 7 sun cimma matsaya za su yi aiki tare don magance matsalar tsaron da yankin ke fama da shi.

Gwamnonin sun ce hakan kawai zai kawo haɓakar tattalin arziki da cigaba na ɗimbin mutanen da ke yankin.

Sun yarda rayukkan da an ka rasa da waɗan da suka shiga matsala da 'yan gudun hijira da aka samu duka sakamakon masu tayar da ƙayar bayan ne.

Gwamnonin sun faɗi haka ne a wurin taron yini biyu da aka shirya kan tsaro a jihar Katsina sun ce sun shirya yin komai domin ganin miliyoyin mutane sun samu rayuwa mai sauki.