Fiye da mutane Miliyan 3.7 na fama da matsananciyar yunwa a arewacin Najeriya-----FAO
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Hukumar abinci da aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan yadda ake fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya,
Inda ta bayyana cewa yara miliyan 3.7 a yankin na fama da tabarbarewar abinci, ko barnatar da su, ko kuma rashin lafiya.
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da kwararre a fannin sadarwa na FAO, David Tsokar, ya raba wa menema labarai a ranar Alhamis.
An bayyana wannan kididdigar ne yayin wani babban taron tattaunawa da gwamnatin jihar Borno tare da hadin gwiwar FAO suka shirya domin bunkasa samarwa da kuma amfani da shirin Tom Brown.
Taron wanda ya gudana a dakin taro na Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja a ranar Larabar da ta gabata, ya hada wakilan ma’aikatun gwamnatin tarayya, masu bayar da tallafi, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyoyi masu zaman kansu, inda suka jaddada aniyarsu na magance matsalar karancin abinci a yankin.
managarciya