Cire Sarkin Musulmi: dokar akwai bukatar a yi takatsantsan---Dan Majalisar jiha
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Isa Honarabul Habibu Halilu Modachi ya ce kudirin dokar da aka kawo a gaban majalisa baya da wata alaka da cire sarkin musulmi amma dai wasu sassan na dokar akwai bukatar a yi takatsantsan sosai kan su domin ganin abin da ke faruwa a Kano, kan haka na gayawa majalisa da ta yi abin da ya dace domin zaman lafiyar jihar Sakkwato.
"tun sanda Sarkin musulmi yake nadawa ba a taba samun wata hatsaniya a kai ba, saboda mi za a sauya tsarin, mutane su kwantar da hankalinsu muna tare da su kuma za a yi abin da ya dace a majalisa.
"Babu maganar cire Sarkin musulmi a majalisa abin da ke nan maganar sarakuna ce da sarkin musulmi ke nadawa yanzu an kawo cewa gwamna ne zai a amincewa Sarkin musulmi, in ka duba a matsayin su na uwaye wannan dan aikin ne dai suke yi, in an ce babu wannan ka ga kamar an cire su ne."
Wasu mutane a jiha na ganin dacewar jingine dokar duk da gwamnatin jiha na ganin da cewar yi wa dokar gyran fuska.
managarciya