NDLEA Ta Kama Hakimi a Sakkwato da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Kama Hakimi a Sakkwato da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

 

Jami’an hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama hakimin garin Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Abubakar Ibrahim mai shekaru 38 kan fataucin kwayoyi. 

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, a Abuja, cewa an kama Ibrahim da ganyen wiwi mai nauyin kilo 3 da kuma kwayoyin exol-5 guda 4,000, Daily Trust ta rahoto. 
Hakimin yana daga cikin mutum 11 da aka kama a tsakanin wasu ayyuka da suka kai jami’an NDLEA ga samo miyagun kwayoyi daban-daban a gadin jihohi bakwai. 
A cewarsa, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja Lagos, jam’an NDLEA da ke aiki da kamfanin shigo da kaya na SAHCO sun kama kwalaye 15 dauke da kwayoyin Tramadol. 
“Yayin da kwalaye 10 na kwayoyin Tramadol 225mg suka fito daga Dubai a jirgin Ethiopia, kwalaye hudu na 100mg da kwali daya na Tramadon 22mg sun fito daga Karachi, Pakistani a wani jirgi daban na Ethiopia."