Sallah: Gwamnan Sakkwato ya ba da umarni Fara biyan Albashin Watan Yuni

Sallah: Gwamnan Sakkwato ya ba da umarni Fara biyan Albashin Watan Yuni


Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto ya ba da umarnin Fara biyan Albashin Watan Yuni anan take ga dukkan Ma'aikatan jiha.
Gwamna Aliyu ya nemi Ma'aikatan su godewa hobbasar ta hanyar rike aikinsu da gaskiya kamar yadda yakamata.
Sanarwar wadda mai magana da yawun Gwamnan Alhaji Abubakar Bawa ya sanar ya ce wannan hobbasar tana cikin alkawain da gwamnan ya yi na kula da walwalar Ma'aikata a jihar.
Ya ce dukkan Ma'aikata da masu karbar fansho za a biya su domin gudanar da bukukuwan sallah cikin sauki da walwalar.