Yakamata A Rushe Jam'iyar APC-----Tsohon Gwamnan Sakkwato
Tsohon gwamnan Sakkwato Malam Yahaya Abdulkarim ya nuna damuwarsa kan rikicin da ya dabaibaye jam'iya mai mulki ta APC ya ce haɗakar da ta samar da jam'iyar yakamata a rushe ta matuƙar manyan jam'iyun da suka samar da APC ba su iya haɗa kan mambobinsu.
A bayanin da ya fitar a Abuja ya ce halin da APC take ciki a yanzu tana iya darewa.
"Manufar samar da jam'iya a siysa don a yi nasara a zaɓe, an yi haɗaka ne aka kafa APC don wannan manufa."
Bayan samun nasara APC ta riƙa samun koma baya har zuwa lokacin da aka kafa kwamitin riƙon ƙwarya, a saman wannan tsarin da ake ana samun ci baya ne in ba a ɗauki mataki ba jam'iyar za ta sake komawa yanda take kowa ya koma gidansu kamar yadda ake baya kafin kafa APC, waton ANPP da ACN da CPC da ɓangaren sabuwar PDP.
"matuƙar aka kasa magance rigimar da ta dabaibaye jam'iyar a soke haɗakar da aka yi wadda ta samar da APC saboda auren da aka yi bai yi alfanu kamar yadda aka yi tsammani ba," a cewarsa.
managarciya