Rigima ta kunno APC, Gwamnoni Shirin Yi wa  Tinubu Zagon kasa 

Rigima ta kunno APC, Gwamnoni Shirin Yi wa  Tinubu Zagon kasa 

Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi barazanar kawowa takarar Asiwaju Bola Tinubu cikas a jihohinsu a 2023. Wani rahoto na musamman da muka samu daga Premium Times a ranar Litinin, ya bayyana cewa ‘yan kungiyar PGF suna jin haushin Bola Tinubu. 

Gwamnonin APC sun fusata ne a kan yadda jam’iyya da ‘dan takararta suka yi watsi da sunayen da suka bada na wadanda za a sa a kwamitin kamfe. 
Gwamnonin jihohi sun samu damar aiko da sunayen ‘ya ‘yan APC biyar da za su shiga cikin kwamitin jam’iyya na yakin neman zaben shugaban kasa.
Abin da ya ba gwamnonin na APC mamaki shi ne, da aka fitar da jerin sunayen ‘yan kwamitin kamfe, sai suka ga an yi watsi da sunayen da suka gabatar.
Kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu sun yi wannan ne ba tare da sanin gwamnonin ba. Wannan ya jawo aka yi ta kai wa APC da PGF korafi. 
Kamar yadda jaridar ta rahoto, Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Ribas yace ba zai ba Tinubu gudumuwa wajen kamfe ba tun da an fi shi sanin jiharsa. Shi ma Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, yace sunaye biyar ya bada, amma sunan mutum daya ya gani cikin mutane bakwai daga jiharsa. 
Abin ya kai su Rotimi Akeredelu suna kai wa jam’iyya kukan an yi watsi da sunayen wadanda gwamnoni suka bada, duk da su suka san ‘yan siyasan ainihi. 
Gwamnonin Arewa maso yamma su na zargin Tinubu bai tafiya da su a takararsa. Sai da sunan ‘yan kamfe ya fito sai abin da suke zargi ya gaskata. Wata majiya tace gwamnonin wannan yanki suna ‘dan takaran ya raina su, kuma idan ya yi sake, za su iya hana shi lashe zabe a Arewa maso yamma.