Kotu Ta Kawo Ƙarshen Takarar Shugaban Majalisar Dattijai  Ahmad Lawan 

Kotu Ta Kawo Ƙarshen Takarar Shugaban Majalisar Dattijai  Ahmad Lawan 

Kotu Ta Kawo Ƙarshen Takarar Shugaban Majalisar Dattijai  Ahmad Lawan 

Kotu ta kawo ƙarshen ja'inja kan wane ne zai yi takarar sanatan Yobe in da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan ya so a kwace kujerar a ba shi bayan ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a jam'iƴar APC.

Kotu ta sanar da Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na Sanata a Yobe ta Arewa. 

A yau, Laraba, Kotun tarayya mai zama agarin Damaturu ta sanar da Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na Yobe ta Arewa karkashin Jam'iyyar APC, tsakanin sa da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawal.

Abin jira a gani ko Ahmad Lawan zai rungumi ƙaddara ya shafa wa kan lafiya ko zai ɗaukaka ƙara don ganin an ba shi abin da nasa ba.