Gwamnatin Sokoto Ta Ce A Shirye Take Ta Yi Tattaunawa Da ’Yàn Bìñdiga

Gwamnatin Sokoto Ta Ce A Shirye Take Ta Yi Tattaunawa Da ’Yàn Bìñdiga

Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa a shirye take ta shiga tattaunawa da ’yan bindiga, matukar suna da niyyar ajiye màķàmansu tare da rungumar zaman lafiya da sulhu.

Gwamnatin ta kuma sake jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, tana mai bayyana aniyar ta na karɓar shawarwari da tattaunawa da kungiyoyin yan bìñđiga da suka nuna shirin juyawa daga hanyoyin tashin hankali.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Gwamna Ahmed Aliyu Shawara kan Harkokin Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya sanya wa hannu, inda ya jaddada cewa tattaunawa da sulhu sun fi amfani fiye da ci gaba da rikici na dogon lokaci wanda ke janyo asara ga rayuka da dukiyoyi.