Bajare Ga Kwamishinan Tambuwal: Ba Ka Cin Rumfarka Kuma Ka Ce Kuna Da Jama'a
Ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jihar Sakkwato Honarabul Malami Muhammad da aka fi sani da Bajare ya nuna mamaki da shakku kan kalaman Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Sakkwato Alhaji Akibu Ɗalhatu a kalamansa da yake faɗi suna da yawan jama'a da ƙarfin gwamnati a jihar Sakkwato.
Bajare ya ce bai gamsu da wannan ba domin shi da ke faɗin suna da yawan jama'a bai taɓa yin nasara a rumfarsa da yake jefa ƙuri'a ba,wanda ke da mutane ya kasa samun waɗanda za su yi masa kara ga wanda yake bi, a duba wannan.
Malami Bajare a hirarsa da manema labarai ya ce rashin aiwatar da abubuwan cigaba ne ga jama'a ya sanya magoya bayan PDP yin soki-burutsu ba kai ba gindi domin ba su da wani abin fadi ga mutanen jihar Sakkwato.
Bajare ya yi wa mutanen jiha albishir matukar APC ta samu nasara za a samu romon dimukuradiyya a fanin ruwan sha da inganta asibitoci da sauran bukatun rayuawa.
managarciya