Gamayyar kungiyoyin Malaman Kano sun yi watsi da sanarwar tsige Sheikh Ibrahim Khalil 

Sannan suka  bukaci al’umma suyi watsi da waccen Sanarwa da aka fitar tun da fari, Sannan Sanarwar tace sun dauki Wannan Matakin ne bisa Amincewa jagororin Qadirriyya da Izala dama Tijjaniya Kamar su: Farfesa Musa Borodo, Sheikh Khalifa Karibullah Nasiru Kabara, Sheikh Abdulwahab Abdullah, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, Farfesa Muhd Babangida , Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Muhd Nasir Adam da Kuma Dr Mu’azzali Ibrahim Maibushira.

Gamayyar kungiyoyin Malaman Kano sun yi watsi da sanarwar tsige Sheikh Ibrahim Khalil 
Gwamna Ganduje
Gamayyar kungiyoyin Malaman Kano sun yi watsi da sanarwar tsige Sheikh Ibrahim Khalil 
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Jagororin gamayya ƙungiyoyin addinin Musulunci na jihar Kano ta yi watsi da sanarwar tsige Sheikh Ibrahim Khalil  Daga shugabancin majalisar malamai 
Hakan na kunshe ikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar Dr. Sa’eed Ahmad Dukawa ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Sanarwar tace wancan Mataki da aka dauka na cire Sheikh Ibrahim Khalil anyi shi bada Sanin jagororin ba, Kuma haka babu abun da zai haifar sai fitina a tsakanin Malamai dama al'umma jihar kano daki daya.
Sannan suka  bukaci al’umma suyi watsi da waccen Sanarwa da aka fitar tun da fari, Sannan Sanarwar tace sun dauki Wannan Matakin ne bisa Amincewa jagororin Qadirriyya da Izala dama Tijjaniya Kamar su:
Farfesa Musa Borodo, Sheikh Khalifa Karibullah Nasiru Kabara, Sheikh Abdulwahab Abdullah, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, Farfesa Muhd Babangida , Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Muhd Nasir Adam da Kuma Dr Mu’azzali Ibrahim Maibushira.
Daga karshe sanarw ta sun tabbatar da Cewa har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil shi suka sani a matsayin shugaban majalisar Malaman jihar Kano domin hakan ne zai tabbatar da zaman lafiyar da ake dashi a Kano.