Gas Din Girki Ya Kara Tashin Gwauron Zabo A Nijeriya 

Gas Din Girki Ya Kara Tashin Gwauron Zabo A Nijeriya 

’Yan Najeriya na kara fuskantar karancin gas din girki, yayin da farashinsa ke ci gaba da tashin gwauron zabo a fadin kasar nan, kamar yadda binciken Aminiya ya nuna.

Rahotanni sun suna tsadar gas din na girki ta fi kamari a garuruwan Legas, Kano, Maiduguri da dai sauransu.

Dillalan gas din girki sun bayyana cewa karancin nasa na dan lokaci ne, kuma hakan ya faru ne sakamakon matsala da jiragen da ke jigilarsa suka samu wajen kawo shi tashoshin riragen ruwa da ke Legas.

Yanzu haka, da dama daga cikin wuraren sayar da gas din giriki ba sa aiki saboda rashinsa wanda za su sayar.

Bincikenmu a gidajen mai da shagunan sayar da gas din girki a sassan jihar Legas ya gano cewa kadan ne daga cikinsu ke sayar da shi, a farashi daban-daban.

A Iyana Ipaja, wakilinmu ya ziyarci gidajen mai guda biyu inda daya ne kawai ke sayar da gas din.

A gidan mai na Petrocam da ke Ile-Epo, Oke Odo, ana ci gaba da sayar da tukunyar gas mai nauyin kilogiram 12.5 kan Naira 12,000 a jiya (Talata).