Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamnan Jihar Ebonyi Da Mataimakinsa Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamnan Jihar Ebonyi Da Mataimakinsa Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

Daga Comr Abba Sani Pantami.

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, a kori Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, bayan sun fice daga jam'iyyar PDP sun koma APC mai mulkin sa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri'u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Mari na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam'iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

A cewar kotun, bayan komawa jam'iyyar APC, Umahi da mataimakinsa, ba PDP kadai suka bari ba, sun raba kansu da kuri'u jam'iyyar ta PDP.

Kotun ta ce idan aka yi la'akari da sakamakon zaben na gwamna, kujerar gwamnan Jihar Ebonyi da mataimakinsa, 'mallakar wanda suka yi karar ne ba wata jam'iyyar daban ba.

"Babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin kasa da ya nuna ana iya musayar kuri'u daga jam'iyya daya zuwa wata jam'iyyar."

Ta ce jam'iyyar PDP ce ke da kuri'un da kujerun da masu zabe a Jihar Ebonyi suka kada, don haka ba za a iya mika wa Gwamna Umahi da mataimkinsa kuri'un ba idan sun fice daga jam'iyyar.