Tambuwal Ya Cancanta Mu Yaba Masa-----Honarabul Bajare

Tambuwal Ya Cancanta Mu Yaba Masa-----Honarabul Bajare
Gov. Tambuwal

 

"Yakamata mu yabawa gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal kan saurarenmu da ta yi kan abin da ya shafi al'umma don kare lafiyarsu da rayuwarsu."

Honarabul Malami Muhammad Galadanchi da aka fi sani da Bajare ne ya furta wadannan kalamai a hirarsa  da Managarciya kan soma aikin kwasar sharar titin Maituta da gwamnati ta soma a yau Talata ya ce Tambuwal ya cancanta a yaba masa kan daukar matakin da ya yi a kiran da muka yi masa na ya kwashe sharar Maituta mun yaba a wannan haujin.

Ya da cewa adawar da ke tsakaninsu da gwamnati ba kiyayya ba ce son gyara ne domin suma 'yan asalin jiha ne duk in da suka fahimci akwai bukatar jawo hankalin gwamnati za su yi domin cigaban jiha,  haka ne dimukuradiyya.
'fatar da nake da ita a wasu matsalolin da muka jawo hankalin  gwamnati su duba su; bayan wannan na shara, kuma wannan halin da aka dauko na saurarenmu don a gyara jiharmu muna fatan ya dore in muka jawo hankalin gwamnati a wasu wurare da muke ganin an kasa a duba su da idon basira.

'Sharar da aka fara kwasa muna fatan kar a tsaya sai an kwashe ta gaba daya don haka ne farincikin Sakkwatawa gaba daya' a cewar Bajare.