Hajjin Bana: Ana Sa Ran Barin  Maniyyatan Najeriya Dubu 15 Gida 

Hajjin Bana: Ana Sa Ran Barin  Maniyyatan Najeriya Dubu 15 Gida 

 

A lokacin da ake bada sanarwar ganin wata, akwai maniyyatan Najeriya da adadinsu ya zarce 15, 000 da har yanzu ba su tafi Saudiyya ba. 

Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta na da mutane jibge a yanzu da ba a kai su kasa mai tsarki ba. 
Akwai maniyyata da-dama da su ke kwana a sansanin mahajjata a dalilin rashin cika alkawarin hukuma da kamfanonin jiragen da ke jigilarsu. 
Hakan ya jawo wasu maniyatta su ka koma kwana a masallatai da cikin farfajiyar filin tashin jirgi. NAHCON ta yi alkawari kowa zai yi aikin hajji.
Rahoton ya ce kamfanin Arik Air ya iya daukar mutane 300 ne daga cikin fasinjoi 7000 da aka ba shi. Hukumar NAHCON ta yi alkawari jirgin saman zai cigaba da jigilar fasinjoji a jiya. Sai dai bincike ya nuna har yanzu fasinjojinsa ba su bar Najeriya ba. Akwai maniyyatan da sun shafe kwanaki biyar su na jiran a dauke su zuwa Saudiyya amma har yau babu labari, hakan zai iya jawo matsala. 
Idan ba a dauki matakan gaggawa ba, maniyatta fiye da 6, 000 ba za su sauke farali a bana ba. 
Dole sai Arik Air ya dauki fasijoji 1, 500 a kowace rana daga yau zuwa lokacin da za a rufe filin jirgin Saudiyya idan ana so a dauke duka ‘Yan Najeriya. Shugaban kungiyar AHUON, Alhaji Nasidi Yahaya ya ce an dauki hayar wani jirgin Max Air domin a iya daukar maniyattan da har yanzu ba su tashi ba. Legit.ng Hausa ta fahimci an kira wasu cikin maniyyata daga kananan hukumomin Kaduna tun Juma’a, amma sai daren yau su ka shiga kasar Saudi.