2023: Sarkin Gwandu Ya Faɗawa Tambuwal Abin Da Yake Son Shugabannin Arewa Maso Yamma Su Yi

2023: Sarkin Gwandu Ya Faɗawa Tambuwal Abin Da Yake Son Shugabannin Arewa Maso Yamma Su Yi
'Yan Bindiga Suna Karɓar Shinkafa da taliya matsayin Kudin Fansa domin yunwa ta kama su a daji

A lokacin da ake tunkarar babban zaɓen 2023 a Nijeriya an nemi shugabanni daga Arewa maso yamma su jingine bambancin siyasarsu domin ɗaurewar haɗin kan da aka san yankin da shi tsawon lokaci.
Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne ya yi wannan kalami a lokacin da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarce sa domin yi masa ta'aziyar rasuwar mahaifiyar daya daga cikin sarakunansa a Birnin Kebbi.

A cewar Sarkin Gwandu akwai buƙatar shugabanni da iyaye a yankin su samar da mafita ga matasa da za ta kawar da su ga aikata abubuwan ɓata gari da ƙwace da barace-barace.
"Ba mu kulawa da tarbiyar ɗiyanmu, mun sake su kawai ga harkar bara abin da addininmu bai yarda da shi ba, sai ka ga yaro a tsakanin shekarru biyar zuwa 10 yana nemawa kansa abinci da ya girma sai koma mai yin ƙwace, yakamata mu farga a matsayinmu na iyaye domin ɗaukar nauyin da Allah ya aza mana, ya ba mu ɗiyan ne don cigaba da kulawa da su.
“Wannan Maharan da suka addabi yankin Arewa, saboda mi a yankin ne yafi shan wahala a ƙasar gaba ɗaya, saboda an watsar da zama 'yan uwan juna." a cewarsa.

Ya yi kira da shugabanni ganin harkar zaɓe na kusantowa da su yi aiki tare don samar da makoma ta gari.