Mahara dauke da makamai sun kashe mutum biyu a lokacin da suke aiki a gona cikin kauyen Sardauna a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato, ba tare da hakkiko wani laifi ba.
A bayanan da aka samu maharan sun kashe manoman a ranar Lahadi data gabata da misalin karfe 3:30 na rana bayan da suka same su a cikin gonakkinsu suna faman aiki domin samun abin da suka ciyar da iyalansu da kansu.
Shugaban 'yan sa-kai('yan banga) dake yankin Musa Muhammad ya bayyana margayan Hamza Na'allah da Zubairu Haruna ne ya ce su uku ne suka je gona lokacin da aka kawo hari dayan ya samu kubuta a wani kauye makwabtansu shi da ajalinsa bai kusa.
Ya ce duk da yanayin da ake ciki na samun zaman lafiya a yankin ana samun kai hare-hare a jefi-jefi cikin wasu kauyukka a kwana hudu da suka gabata sai da aka dauke wasu mutum hudu a kan hanyar Sabon Birni zuwa Goronyo.
An kuma dauke wasu mutum 20 bayan da suka dawo daga Mauludin Inyas a jihar Zamfara.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Sakkwato ASP Sanusi Abubakar an kasa samunsa domin sanin halin da ake ciki a yankin da matakin da aka dauka.