Mutum 57 'Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Kwana 2 A Sakkwato

Mutum 57 'Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Kwana 2 A Sakkwato
Mutum 57 'Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Kwana 2 A Sakkwato
Mutum Hamsin da bakwai ne 'yan bindiga suka kashe cikin kwana biyu a jihar Sakkwato a harin da aka kai a karamar hukumar Goronyo da Ilela da Sabon Birni.
A bayanin da ake da shi an kashe mutum 43 a Ilela, sai 14 a karamar hukumar Sabon Birni.
Harin da aka kai na baya da aka kashe mutum 14 ya zo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na yakar mahara da suka addabi jihar.
Mutanen Sabon Birni sun tabbatar da harin da aka kai a unguwar Lalle da daren ranar Talata, in da suka kashe Usman Abdullahi Unguwar Lalle, suka tafi Tsangarewa suka kashe mutum Tara, daga nan suka tafi Tamindawa suka kashe hudu, haka ma sun yi harbi kan mai uwa da wabi ga motar jigila a kauyen Gajid sun kashe mutum uku har da direban mota, mutum biyar sun samu rauni halin yanzu suna karbar magani a asibiti.
'Yan bindigar sun yi garkuwa da mutum uku a kauyen amma an sake su bayan biyan fansar miliyan 2.