Yadda 'Yan Majalisar Shura Ta Shekarau Suka Raba Naira Miliyan 100 Da Atiku Ya Ba Su

Yadda 'Yan Majalisar Shura Ta Shekarau Suka Raba Naira Miliyan 100 Da Atiku Ya Ba Su

Wasu hotuna sun nuna wasu mambobin Shura, majalisar shawara ta harkar siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, suna raba wani kaso na Naira miliyan 100 da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar domin tara magoya bayan jam'iyyar a ziyarar da ya kai Kano.

Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya yiwa shugabannin PDP na Kano wanka da kuɗi har naira miliyan 130, inda Malam Shekarau ya samu kaso mafi tsoka na  Naira miliyan 100, shi kuma ɓangaren Aminu Wali ya samu Naira miliyan 30.

A karshen watan Agusta ne dai Atiku ya ziyarci Kano domin karɓar Malam Shekarau, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP ta Rabiu Kwankwaso zuwa PDP.

DAGA Salisu Magaji Fandalla'fih