Isah Sadik Achida Ya Samu Nasara A Kotun Ɗaukaka Ƙara

Isah Sadik Achida Ya Samu Nasara A Kotun Ɗaukaka Ƙara


Kotun ɗaukaka ƙara da ta yi zama a Abuja ta gabatar da hukunci in da ta jingine hukuncin kotun farko  da ta baiwa Mainasara Sani nasarar zama shugaban jam'iyya a Sakkwato.
Ɓangaren Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da ke da mafi awan magoya baya a jam'iyar APC ne suka zaɓi Isah Sadik Achida matsayin shugaban jam'iyya a jiha.
Gefen Sanata Abubakar Gada suka aiyana Mainasara Sani ne shugaba, abin da ya haifar da garzayawa  kotu daga mutanen Abdullahi Balarabe Salame domin a dakatar da Mainasara ya bar kiran kansa shugaba.
Gabatar da hukunci a kotun ɗaukaka ƙara Alƙali Haruna Simon Tsammani ya soke hukuncin farko da babbar kotun Abuja ta yi saboda ba ta da hurumin sauraren shari'ar in da ta aiyana Mainasara ne shugaban APC a Sakkwato.
Alƙalin ya ce kotun Abuja ba ta da hurumin sauraren lamarin da ya faru a Sakkwato, yakamata a riƙa lura a daina kawo masu irin waɗan nan lamurra.
Lauyan Achida Dakta Hassan Liman ya jinjina kan hukuncin tare da cewa zai bayar da rahoton lauyan da ya kawo shari'a ba a kotun da yakamata ba.
Wannan hukuncin ke nuna Isah Achida ya samu nasara a shari'ar ganin kotun ta aminta da ya shiga shari'ar wadda ba da shi aka fara ba, kuma ta soke hukuncin farko na kotun Abuja da ta aiyana Mainasara a matsayin shugaban APC a Sakkwato.


c