'Yan adawa ne suka yi zanga-zanga a Sakkwato---Gwamna Ahmad Aliyu

'Yan adawa ne suka yi zanga-zanga a Sakkwato---Gwamna Ahmad Aliyu

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya zargi magoya bayan wasu jam'iyyu da ba nasa ba ne suka kitsa zanga-zangar neman karshen mulkin zalunci da aka yi a jihar a satin da ya gabata.
Zanga-zangar da aka yi a fadin Nijeriya domin an karar da shugabannin halin da talaka yake ciki na ƙunci da rashin tabbas wadda matasan suka shiga gwamnan ya zargi 'yan adawa da kitsa ta jiharsa.
Gwamna Ahmad Aliyu a jawabin da ya yi a fadar gwamnati kafin soma taron majalisar zartarwar jiha a Laraba ya ce an yi zanga-zanga ba kashe kowa ba, ba a sace kayan kowa ba, haka ba wanda aka yiwa rauni ita ce zanga-zanga mafi tsafta a Nijeriya.
"A tunanin da nake da shi 'yan adawa ne suka shirya ta domin su lalata kayan gwamnati da aka samar, saboda  ba su jin dadin yanda aka kawo cigaban jihar ta hanyar zamanantar da jiha,"kalaman Gwamna.
Ya ce 'yan adawa ba za su yi nasara ba domin samar da cigaba tafiya ta yi nisa sosai.
Masu sharhi kan lamurra a jihar Sakkwato na ganin kamar daura lamarin zanga-zanga ga 'yan adawa, gwamna bai yiwa mutanen jiha adalci ba, in aka duba yadda mutane suke cikin bakin talauci da tsadar rayuwa a jiha, abin da ake zargin gwamnati da yiwa lamarin rikon sakainar kashi.
A birnin  jihar Sakkwato 'yan gudun hijira sun cika shi sosai, gidajen da ke dafa abinci a yini su ne kadan yunwa ta shiga gidaje da yawa a jiha, wadannan dalilai ya sa mutane suka fito don nuna rashin gamsuwarsu da tsare-tsaren gwamnati, su ne yakamata gwamna ya duba don yin wani abu ba tsayawa sukar wadanda suma 'yan jiha ne suna da hakkin nuna matsayar su ga tafiyar gwamnati.