Rikicin PDP: Atiku Ya Yanke Shawarar Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba

Rikicin PDP: Atiku Ya Yanke Shawarar Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba


A yau Litinin 10 ga watan Oktoba, 2022, babbar jam'iyyar hamayya PDP zata buɗe yaƙin neman zaben shugaban ƙasa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Jaridar Vanguard ta gano cewa da yuwuwar dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yanke hukuncin fuskantar abinda ke gabansa da Wike ko babu shi.

Wasu bayanai daga wani na ƙusa da Atiku sun nuna cewa mafi yawan mambobin jam'iyya sun yi watsi da kiraye-kirayen da gwamna Wike na Ribas da yan tawagar ke yi na shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya yi murabus. 
Bugu da ƙari, jagoran tafiyar Ward2Ward4Atiku, Abraham Chila, ƙungiyar da ke kokarin tattara wa Atiku mutane tun daga tushe, yace arewa ta tsakiya ba zata yarda a sauke Ayu ba. DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka A cewarsa, shugaban PDP na ƙasa ba zai sadaukar da kujerarsa ba kamar yadda Chief Audu Ogbeh, ya yi lokacin da aka tilasta masa sauka daga jagorancin PDP a baya. Legit.ng Hausa ta tattaro cewa hakan ya biyo bayan ƙarin bayanan da ake samu kan yadda mambobin kwamitin ayyuka (NWC) da ma'aikata suka yi kashe mu raba na biliyan N1.3bn alawus ɗin gida. 
Atiku da Wike sun jima ba su ga maciji kan bukatar sauke Ayu daga mukaminsa. Hakan yasa wasu kusoshin PDP suka tsame hannu daga tawagar Kamfe kan ƙin saukar Ayu. 
Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa Atiku da makusantansa sun yanke ci gaba da harkokin kamfe ba tare da gwamna Wike da sauran masu mara masa baya ba.