KOTUN KOLI TA SANYA  RANAR SAURAREN KARAR ZABEN GWAMNAN SOKOTO

KOTUN KOLI TA SANYA  RANAR SAURAREN KARAR ZABEN GWAMNAN SOKOTO

Kotun Kolin Nijeriya  ta sanya ranar Laraba  domin sauraren karar zaben Gwamnan Jihar Sokoto wadda  dan takarar gwamna na jam'iyar PDP a jihar Sokoto Malam Sa'idu Umar Ubandoman Sakkwato yake kalubalantar  sahihancin zaben  Gwamnan Jihar Dakta Ahmad Aliyu Sokoto  a Kotun kolin.

Kotun ta bayyana cewar zata fara zaman sauraren karar ne a harabar  kotun da misalin karfe 9:00am na safe a ranar ta Laraba 17 ga Watan January, 2024.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan Sakkwato a gefen kafofin sada zumunta na zamani Hon. Naseer Bazza ne ya fitar da bayanin na soma Shari'ar da ke cike da rudani in da kowane bangaren jam'iya APC da PDP ke ganin suna da gaskiyar da za ta sanya su yi nasara.