Kotu ta Rusa Zaben Fidda Gwani Na Gwamna A Jam'iyar APC  Adamawa 

Kotu ta Rusa Zaben Fidda Gwani Na Gwamna A Jam'iyar APC  Adamawa 

 

 

Daga Ukasha Ibrahim.

Kotu ta rushe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa wanda Nuhu Ribadu yashigar da kara  inda yake kalubalantar nasarar da Senata Aisha Binani  tasamu na lashe gwani a zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyar APC.

 
Mai shari a justice AbdulAziz Anka wanda shine ya jagorancin shari ar  ya karanto tuhume-tuhumen da kuma hukuncin da kotu ta yanke  ne kamar haka :
 
1. Batu kan amfani da kudi yayin zabe :
 
Kotu ta yi watsi da maganar da ake cewa "yar takarar Gwamna senata Aisha Binani tayi amfani da kudi  domin juya zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyar APC
 
2.  Batu amfani da kudi domin sayan masu kada kuri u daga karamar hukumar Lamurde:
 
Kotu tayi watsi da hujjojin da bangaren masu kara suka gabatar gareta na cewa "yar takarar gwamnan jihar Adamawa senata Aisha Binani tayi amfani da kudi wurin sayan masu ka'da 'kuri u na Karamar hukumar lamurde 
 
3 . Batu kan aringizon kuri u a yayin zabe :
Mai shari a AbdulAziz Anka yace wanan matsala ce daga wurin masu tantance  masu 'kada kuri u  ba laifin "yar takara senata Aisha Binani bane 
 
A karshe dai kotun tarayya dake Yola fadar jihar Adamawa karkashin jagorancin mai Shari a AbdulAziz Anka ta rushe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Adamawa wanda jam'iyar APC  ta gudanar sanan ta bada umarnin sake yin sabon zabe anan da sati 2 masu zuwa