Buhari Ya Yi Zaman Sirri Tare Da Wamakko da Tinubu Da Sauran Jagororin Da Aka Kafa Jam'iyar Da Su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cigaba da tuntuba da masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC kan babban taronsu da za su yi ranar Assabar ya karbi bakuncin jagororin jam'iyar da aka kafa APC da su.
Wadanda da suka halarci zaman akwai jagoran jam'iyar APC a Nijeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; da shugaban jam'iyar na farko Chief Bisi Akande; da ministan kimiya da fasaha Dakta Ogbomnaya Onu; da tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha; da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau; da tsohon gwamnan Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko[Sarkin Yamma Sakkwato].
Sauran su ne : Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna); Aminu Masari (Katsina) da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Haka ma shugaban rikon kwarya na jam'iyar Mai Mala Buni da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, sun halarci zaman.
Haduwar wadda aka yi da shugaban kasa an yi ta ne domin ya gode masu da irin rawar da suke takawa a goyon bayan da suke ba shi da fahimta da hadin kai ga gwamnatinsa.
Zaman an yi shi ne kuma domin samar da maslaha a yi zaben jam'iya ba wani rigima.
Har yanzu fadar shugaban kasa ba ta fitar da bayanin zaman ba domin an yi shi a asirce.
managarciya