Idan ba mu yi ƙarin farashi ba to za a ga ba daidaiba - Masu kamfanonin sadarwa

Idan ba mu yi ƙarin farashi ba to za a ga ba daidaiba - Masu kamfanonin sadarwa

Masj kamfanonin sadarwa ta waya da data sun bukaci a yi nazari cikin gaggawa game da farashin kiran waya da na data duba da yanayin da tattalin arziki ke ciki don dorewar kamfanonin nasu.
 
Idan ba haka ba, sun ce ba za su iya tabbatar da ingantaccen aiki ga masu amfani da wayoyi ba saboda matsalar tattalin arziki da su ke fuskanta.

Shugaban kungiyar masu harkokin sadarwa ta kasa (ALTON) Engr Gbenga Adebayo ne ya yi wannan kira a madadin daukacin kamfanoni a wani taro na karshen shekara da masu ruwa da tsakin masana’antu suka shirya a Legas a ranar Lahadin da ta gabata, sannan su ka fitar da sanarwa a jiya litinin.

Daily Trust ta rawaito cewa Adebayo ya ce harkokin su na neman durkushewa kuma dole ne a yi ƙarin farashi cikin gaggawa domin kaucewa durkushewar bangaren.