Fasinjojin Jirgin Sama Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Sun Yi Hatsari

Fasinjojin Jirgin Sama Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Sun Yi Hatsari

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Wani jirgin fajinja dauke da mutane 30: ya fadi dai-dai lokacin da yake shirin sauka a filin jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar Somalia, amma babu wanda ya rasa ransa, 

 
Sai dai kuma babu wanda ya rasa ransa cikin dukkanin mutane 30 din da ke cikin jirgin da wani fai-fan bidiyo da ya rika yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jirgin ya tuntsire a kokarin da yake yi na saukar gaggawa, 

 
Bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya yayin da masu aikin kashe gobara suka fara aiki cikin gaggawa don kashe wutar da ta tashi a jirgin lokaci guda kuma ana kokarin zakulo mutanen cikin jirgin, 

 
Bayanai na cewa tuni aka garzaya da fasinjojin asibiti don ba su agajin gaggawa yayin da aka fara tattara bayanan dalilin saukar gaggawar jirgin, 

 
Jirgin na Jubba Airways ya taso ne daga garin Baidoa zuwa babban birnin kasar Mogadishu kafin ya yi hadarin a filin jirgin saman.