Yadda Kauyuka 50 Suka Watse da Turji Ya Yi Barazana, Jigon APC Ya Shawarci Tinubu 

Yadda Kauyuka 50 Suka Watse da Turji Ya Yi Barazana, Jigon APC Ya Shawarci Tinubu 
Tsoron rashin tsaro ya mamaye garuruwan Zamfara yayin da aka sanar da cewa fiye da kauyuka 50 a yankin karamar hukumar Shinkafi sun zama kufai. 
Wannan hijira ta faru ne sakamakon tsoron barazanar da dan bindiga, Bello Turji ya yi ga kauyukan. 
Jigon APC, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a Gusau, cewar jaridar Vanguard. 
Hakan ya biyo bayan bidiyon da Bello Turji inda ya gargadi hukumomi cewa zai kai hari a Shinkafi, Zurmi, da kuma Isah, idan ba a saki ɗan uwansa, Bala Wurgi, da aka kama ba. 
Ya yi wannan barazana ne a ranar Larabar 25 ga watan Disambar 2025 da ta gabata, yana mai cewa lokaci yana ƙurewa kafin ƙarshen shekara. 
Dr. Sani Abdullahi ya ce tun bayan fitar bidiyon Turji, fiye da kauyuka 50 a Shinkafi sun zama kufai.
Wannan matsalar hijira ta nuna yadda rashin tsaro ya ƙara muni a yankin, inda al'umma ke kira ga gwamnati ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.