An Yi Wa Yarinya ’Yar Shekara 10 Kisan Gilla a Birnin Kebbi

An Yi Wa Yarinya ’Yar Shekara 10 Kisan Gilla a Birnin Kebbi

Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an yi wa wata yarinya ‘yar shekara 10 mai suna Glory kisan gilla a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi.
Wani makwabcinsu a unguwar Badariya ya shaida cewa kallo na karshe da aka yi wa yarinyar shine lokacin da take wasa a wajen gidansu sai mahaifiyarta ta ce ta je ta share mata daki. 
Ya cigaba da cewa, a lokacin da yarinyar ba ta dawo kan lokaci ba, sai mahaifiyar ta aika kanwarta mai kimanin shekara biyar ta kira ta. 
Lokacin da kanwarta ta shiga dakin sai ta same ta tana rike da wuyanta da igiya an shake ta da karfen tagar dakin Mahaifiyar yarinyar ta ce yadda aka kasheta ya zo musu da mamaki. 
Saboda babu wanda ya yi tsammanin za a yi kisan gilla ga yarinya mai wannan shekarun na ta. 
Mahaifiyar ta tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda domin bincike da daukan matakin da ya dace. 
Sannan kuma an kai gawarta kauyen iyayenta da ke karamar hukumar Zuru domin binne ta a can. 
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba.