HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amna Mafi Muni, Fita Ta Sha Huɗu

HAƊIN ALLAH:Labarin Soyayya Da Cin Amna Mafi Muni, Fita Ta Sha Huɗu

HAƊIN ALLAH

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)*

            Page 14


Ganin na ƙafe gun, bakina ya kasa ko motsawa ya daka min tsawa da muryar takaici yace, "To wallahi ba zan iya bar maki nawa kuɗin ba, kuma ni ba ɗan aike bane balle ki tasani gaba da aikenki wacece ke? Idan za ki ban kuɗi duka ki ban kawai na gaya maki ban da kuɗi ne da ina da su me zan ci da Naira ɗari biyar ɗin ki ɗin banza." 
Ganin dai idan ba da gaske nayi ba tabbas ba zan samu ɗari biyar ɗin tashi ba nima tawa ta shige don haka nace cikin muryar son yi kuka nace, "Don Allah ka rufa min asiri karka amshe kuɗin nan duka, domin kaga mutane zaune tsabar gida, suna jiran a basu aiki kuma babu abin da aka samu aka basu, don Allah ka taimaka ka ara min taka ɗari biyar ɗin gobe idan na samu sai na maido maka abinka." Wani kallon galala ya bini da shi, kamar ya kife ni da mari yace, "Ke amma dai kin ci kai ko? Ni nace daman ki tara mutanen? Ban da shegiyar gulma daman miye na tara min mutane cikin gida kamar uban wani yaban ajiyar abin da zan ba su? To tun kafin ranki ya ɓaci ma ki je ki cewa kowace magulmaciyar mace ta fice min daga gida babu abin da zan kawo na aiki Ni, idan kuma ki kai shiru ke za ki ji kunya cikin mutane."

Hawaye suka zubo min ban haƙura ba nace, "Don girman Allah kai haƙuri ka bar min nawa kuɗin to sai na samu ko ruwa ne na siya kafin muga me anjima zatai don Allah." 
Tsaki ya yi ya amshe dubun ya saka a aljihu yace, "Ke dai ce abar ji ke sauran jaje ya rage wa."
Ficewa ya yi ya barni gun na daskare hawaye na zubowa a idanu na, ji nake me yasa ma kasance a raye? Me yasa ban sake guduwa ba kamar yadda muka gudu daga Iyami? Me yasa na zauna gidan Deeni har na samu ciki ? Me yasa ban bi duniya ba? Tabbas nayi ma kaina babban rashin kyautawa tunda har na kai matsayin aje yaro ina zan je kuma yanzu?" Kukan gaske ya zo min har na falo na jiyo sautin kukana. Ko ban faɗi ba nasan matan unguwarmu sun samu abin tattaunawa a cikin unguwa a haihuwar... "Jiddah me ye abin da ya yi zafi za ki zauna nan ki dinga rusa kuka ke da Allah Ya azurta da samun kyautar ɗan mutum?" Yayar mahaifiyata ce ke min maganar, ta jima tana min nasiha, muna cikin hakan muka ji mutane na cewa "Oyoyo ga mutanen Kano."  Ni da Inna bamu san wa ya riga fita ba wajen ba domin mun fahimci Hajjo ce ta zo.
Yara ke ta shigowa da kayan abinci da kayan miya da abubuwa iri-iri kamar daga sama. Ban sake tsinkewa da lamarin ba sai da naga an shigo da buhun shinkafa buhun dawa buhun gero buhun fulawa da jarkar manja data farin mai , hatta magi kala-kala aka shigo da su. Sai da aka gama shigowa da komai sannan Hajjo ta shigo ɗauke da akwatin kaya da ƙatuwar leda . Mutane nata yi mata sannu, nikam tashi nayi da gudu na afka jikinta na fashe da kuka mai taɓa zuciya.  "Haba Jiddah miye na kukan kuma tunda ga Ni? Kin san ban san kina kuka ko? Share hawayenki ki amshi saƙon Uncle Salim ɗinki."  Ai kukan kamar ƙara turomin shi ake baki ɗaya kukana ya saka jikin kowa sanyi harda Hajjon itama ta fara share hawaye tana cewa, "Ki dai ƙara haƙuri Jiddah Allah na nan bai manta da ke ba, tabbas gaba sai kin ba kowa mamaki." 
Sai da Hajjo ta ga na natsu sannan ta buɗe akwatin kayan jarirai ne masu kyau da tsada har da pampas ƙaton gaske, ledar kuma atamfofi ne da leshi tare da shadda dukkansu a ɗinke suke. Hajjo ta dube ni tace "Wannan in ji Uncle Salim ɗinki yace yana gaida ki sosai." Nan da nan akai ta ɗaga kayan ana saka albarka, Hajjo ta fice waje ta dinga ware kayan da duk za ai amfani da shi nan take ta fasa buhun shinkafar ta ɗiba tace a ɗora girki duk ga mutane zaune ana aikin ana cin abinci ai aikin yafi daɗi da sauri. 

Nan da nan kuwa gida ya cika da mutane ana ta aikace-aikace kamar ranar sunan ma. 

Baƙin cikina ya kau, komai ya zama tarihi na ɓangaren kayan abinci da kayan da za mu yi fitar suna Ni da Yarona. Sai tunanin abin yanka ya dawo ya yi min zaune a cikin zuciyata don haka sai jikina ya yi sanyi don banga alamar Deeni zai yanka min ko bindi ba balle Rago ko Akuya. Hajjo ta jani inda ba mutane tace, "Jiddah Mahaifiyarki ta kirani a waya ta gayamin halin da kike ciki duka, tabbas na girgiza sosai me yasa dangin mahaifinki basu da tunani ne? Me ye amfanin yi maki aure da wanda bai da tsayayyen aiki ko sana'a? Me yasa basu dinga taimakonki tunda su sukai maki auren? Yanzu me ya rage ba ai ba na hidimar sunan?" Cikin ajiyar zuciya nace "Babu abin yanka (Rago) don ban ganshi ba haka bai min maganar akwai ko babu ba."  Hajjo ta girgiza kai tace, "Wannan kuma shi ta shafa kada Allah Yasa ya yanka ai yaronsa zai mawa ba ke ba, don haka mu bai shafe mu ba, kece tamu don haka ba zamu bari ki wulaƙanta ba duk rintsi don haka na soyo maki naman rago nayi maki dambun kaza ga kwalin kifi can da za a yi amfani da shi cikin alala gobe da kwai shi ne damuwarmu, kuma na siyo kayan abincin can ne da kuɗaɗen da iyayenki (yaran Hajjo) suka bada a kawo maki, yanzu haka akwai Naira dubu ashirin a gurina wadda za ki kama sana'a bayan suna zamanki a haka ba zai yiyu ba, Jiddah ita rayuwar aure da kike gani ta gaji ɗaci da bauri tare da zuma mai cike da zaƙi, ina son ki ci-gaba da haƙuri da rayuwa ki jure watarana sai labari, Jiddah ina ji a jikina za ki zama abar kwatance abar alfahari a cikin dangi da jama'a ko'ina sai anyi alfahari da ke Jiddah insha Allah." Tunda ta fara magana nake share hawayena ina jin inama maganarta ta tabbata? Amma ta ina hakan zai faru? Na kasa ma cika burina na samun zama cikin aminci da walwala ko da hakan na samu zan farin ciki, so nake naga rayuwar aurena tamkar  yadda nake ganina a mafarki tare da wanda ban taɓa ganin ko da fuskarsa ba, so nake naganmu muna tsokanar juna, muna kiran juna da sunayen soyayya irin su Prince da Princess ko King da Queen, amma yaushe zan samu hakan? Deeni sam bai iya rayuwar farin ciki ba, ko da yake ban sani ba ko nice bai son mu yi rayuwar farin cikin da shi tare ba, idan ba haka ba komai nakan yi shi kan ƙa'idarsa yadda yake so, amma shi sam ko a jikinsa babu abin da yake birge Deeni irin yaga hawayena, yana son ganina ina kuka yana farin ciki ya ganni cikin damuwa ban san me yasa hakan ba sam... "Ke Jiddah ba naji ance kina da hawan jini ba? Amma kuma kike tunani irin wannan? Tun ɗazun nake magana amma hankalinki sam bai gurina kin lula duniyar tunani? Don Allah ki kiyaye lafiyarki Jiddah ko don gaba ki ji daɗin yin sabuwar rayuwarki cikin aminci kin ji?" Ɗaga mata kai nayi, amma har ga Allah tunani nake yaushe ne ma zan daina tunani bayan kullum sai abin tunanin ya same ni? Don haka jin Hajjo kawai nake nasan baƙin ciki ne ajalina kawai.

           RANAR SUNA ***

Tunda asuba kowane magidanci wanda ya samu ƙaruwa ke tashi ya yi wanka ya kimtsa ya saka sabbin kaya don zuwa gun raɗin sunan ɗansa, amma ban da Deeni yana ɗaki kwance yana sheƙa barci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, duk abin da za a ɗauko a cikin ɗakin sai dai na je na ɗauko, tabbas ya takurama mutane da dama barcinsa amma wa ya isa yace ya tashi ya fice? Amsar ita ce, babu shi duk gidan nan. Ina jin wayarsa na ƙara ita ce ta tada shi daga barcin da yake, muna jin shi yana cewa ba zai samu zuwa ba amma a saka sunan yaron Aliyu. Ajiyar zuciya nayi tabbas haka sunan da Safiya ta gaya min yace mata zai sama yaron kenan, Allah Sarki! Wai Safiya ta fi ni muhimmanci a gun mijina Uban ɗana? Babu komai akwai Allah.
Maza ne da dama suka dawo daga raɗin suna dangin mahaifiyata sunata sama yaron albarka, nan da nan aka fitar masu da koko da ƙosai tare da tuwon da aka bi dare aka yi daman don hakan.

Sai da gida ya cika ya batse da mutane sannan Deeni ya tashi ya fito, ba kunya ba tsoron Allah ya ɗauki buta ya shige kewaye (toilet) ya fito ya wanke jikinsa inda ya saba wankewa ya shige ɗaki ya sauya kaya ya ƙwaɗa min kira.
Ina zuwa ya dubeni fuska murtuk yace, "Dame-dame akai ne na abincin sunan?" Cike da fara'a nace, "Akwai alala, shinkafa, tuwo, dambu."  Ya taɓe bakinsa yace, "Babu soɓo da dinja kenan?" Ina murmushin Yau abin da armashi nace, "Duk za a yi su, har da kunun aya ma za ai don an kai markaɗe ma yanzu haka." 

Ya jinjina kansa, "To saura kada ki samu manyan kuloli ki zuba min ni da abokaina ki aje zan aiko a amsa, kuma naga nama can a kuloli ki tabbatar kin zuba min mai yawa, kar ki manta ki zuba mai yawa a kaiwa ƙawarki Safiya Yau na huta da bata kuɗin abinci." 
Jin Deeni ya halakar da Ni, yasa na kasa magana sai kawai kaina na ɗaga ma shi tamkar ƙadangaruwa. Jiki sanyaye na dawo cikin mutane ina mamakin halin Deeni da ƙarfin zuciyarsa, bai bada ko sisi ba amma ji yadda yake ban umarnin abin da yake son nayi ma shi, ba wannan ne ya ban mamaki ba illa irin umarnin daya ban kan Safiya, watau shi ke ci da ita kenan ma yanzu amma ko a jikinsa ya barni a zaman yunwa da wahala ga ciki na haihu ya kasa buɗe bakinsa ya yi min ko da sannu ce balle ya yaba min abin kirkin da nayi na haifar masa ɗan fari.
Nan inda nake daskare ya raɓa ni zai wuce ya dawo kuma yace, "Ɗan ban dubu biyu nan ma tunda nasan dai kin fara kamawa naga danginki sai wani ɗaure-dauren fuskar banza suke tunda dai ba su ne suka ban aurenki balle suce na sake ki ba." 
Haka na buɗe jakar hannuna na ɗauko kuɗin na ba shi ya amsa bai ko waigo ba ya fice daga ɗakin, ina jin mutane na gaida shi suna mai barka da murnar an raɗa suna.

Cikin ikon Allah akai taron suna mai ban mamaki domin mutanen gari sun yi min kara sosai wadda ban taɓa zato ba, na samu alheri iyakar alheri ga kayan jarirai ga atamfofi ga kuɗi ga kayan abinci komai alhamdulillah!
Da dare bayan kowa ya watse Hajjo tace a rufe gidan Yau Deeni bai kwana gidan duk rashin kunyarsa, sai da gabana ya faɗi jin maganar Hajjo, domin nasan wani sabon tashin hankalin ne zan afka idan suka tafi suka barni da Deeni.
Ya kuwa dawo yaita buga gidan, Hajjo da kanta ta leƙa tace , "Kai Deeni wai mu ɗin sa'anninka ne? Koko akwai sa'arka a cikinmu ne? Ban san rashin kunya maza ka ba mutane waje tunda baka san abin da kake ba." Ta maida gidan ta rufe ta barci a tsaye yana kallonta.

Ta dawo tana ta faɗa tana cewa da nan garin nake sai na saka iyayenta sun gyara mai zama wallahi shegen yaro ko kyan kirki babu sai rashin kunya da rashin sanin darajar mutane, ban san uban da ya yi ma shi jagorancin auren yarinyar kirki irin Jiddah ba." 
Nan fa mutane kowa ya yo caaa! Da abin da yake cewa,kowa na faɗin kalar rashin darajar da Deeni ya yi a gabansa. 
Ni dai Salati kawai nake ina neman mafita gun Ubangiji kan abin da Hajjo ta jawo min Yau.

Sun jima suna ta ban shawarar na daina nuna mai tsoro na daina barinsa yana taka ni na zama mace na nuna mai nasan ciwon kaina idan ba haka ba kasheni zai a banza ya auro wata hankalinsa kwance. Ni dai jinsu kawai nake ban jin na ɗauki shawara guda a gunsu.
Bayan sun gama maganar Deeni aka fito da duk abin da na samu aka ƙirga kuɗi Naira dubu arba'in da takwas da canji , sai turmin atamfa guda goma sha ɗaya kayan jarirai ne ba a ƙirga ba, saboda ance yaron dama bai da kaya.
Hajjo ta dube ni tace, "Jiddah yanzu wane shawara kika yanke akan kuɗaɗenki? Zannuwan dai dama an gaya min an sace maki kayan lefe don haka ki aje abinki a hankali ki dinga ɗinka abin ki tunda Allah Ya baki miji mugun gaske wanda bai san haƙƙin aure ba, sai ki cire kala biyu ki ba da a kaiwa Mahaifiyarki ita ma ta ƙara tunda tana da buƙata itama, kuɗinma ki bata wani abu daga ciki sai ki samu sana'ar kirki ki fara yi saboda ki samu abin da za ki riƙe kanki da yaronki."

Kowa ya yi na'am da shawarar Hajjo, don haka na cire dubu goma sha biyar nace akaiwa mahaifiyata na ba Inna data zauna min dubu biyar na adana sauran kuɗin, zannuwan ma kala biyar na bata amma akace na bata uku nace a bata huɗu Inna ta ɗauki gudan.

Washegari suka gyara min gidana fes suka wuce ina kuka Hajjo na kuka suka barni da wata tsohuwar da Hajjo tasa aka kira ta dinga zuwa safe da yamma tana ɗora min sanwar ruwan wanka tana yi ma yaron wanka kullum har mu yi arba'in.

Sai yamma lis Deeni ya shigo gidan cikin matuƙar ɓacin rai da fusata tun daga bakin ƙofar gida yake ƙwaɗa min kira.

Mu haɗu a kashi na gaba don jin yadda zata kaya tsakaninsu .
Wace irin sana'a Jiddah zata yi?
Wane irin mataki Deeni zai ɗauka kan Jiddah?

Taku a kullum Haupha!!!!