WATA UNGUWA: Fita Ta 35
Cikin azama Iya ta janye kwanon abincin gefe tana faɗar "Sannu sannu karɓi ruwa ki sha." Ta miƙa mata kofin ruwa ta ɗaga ta shanye tas amma har zuwa lokacin tarin bai sake ta ba. Dakyar aka samu ta dawo hayyacinta ta ƙarasa cin abincin. Wannan dalilin ne ya saka bata sake magana ba har ta ƙarasa cin abincin. Za ta miƙe ta fita kenan yayarta Zam'atu ta shigo ɗakin riƙe da ledoji manya-manya guda biyu.
BABI NA TALATIN DA BIYAR
Inna Halima tana nan tsaye ta sandare tamkar itaciyar da aka dasa, numfashinta sai sauri yake ƙarawa ganin za a salwantar mata da yaro.
Cikin baƙin nufi Shu'aibu ya sake ƙafar yaron ya fara tafiya zuwa cikin rijiyar yana ihu "Wayyo mama! Don Allah a taimake ni."
Yayin da jama'ar da ke wurin suka rafka salati
Take maganan Halima suka fara gani dishi-dishi sai wani negative take gani tamkar talabijin ɗin da aka joganewa area. Hawaye ya fara tsere a kan ɓula-ɓulan kumatunta.
Wani matashi mai azama da zafin nama ne ya yi hanzarin riƙo ƙafar Anas ta dama yana ƙoƙarin janyo shi. Ganin hakan ya saka wasu daga cikin jama'ar wurin suka tallafawa burinsa na ceton wannan rayuwar. Sai ga Anas sun janyo shi yana haƙi.
Suna ajiye shi ya ranta a na kare a matuƙar tsorace har yana shessheƙa ya nufi hanyar gida. Ita ma Halima ganin hakan ya saka ta saki doguwar ajiyar zuciya tare da miƙewa ta bi bayansa cikin hanzari. Tana shiga gidan ta datse ƙofar daga ciki.
A ranar bata samu damar komawa majalisar tasu ta magulmata ba tsabar firgicin da ta shiga.
Ita kuwa Iya mai bakin Aku koda ta fito da goro a hannunta tana washe baki bata ga Halima ba. Cikin mamaki ta kalli Sagira da ke tsaye wurin tana jiranta.
"A'ah! Ina Haliman ta je ne ba ko sallama?"
Sagira ta yi wani shu'umin murmushi ta ce "Yanzun nan wani yaro ya shigo a guje yake labarta mata mummunan aikin da Anas ya aikata wa abokinsa shi ne ta fice da hanzari."
"Bangane ba 'yar nan fito mini a mutum, me Anas ɗin ya aikata?"
"Kisan kai." Sagira ta sake bata amsa cikin murmushi da alama abin da ya farun ya yi mata daɗi.
Iya ta dafe kirji da hannayenta tana fito da ƙananun idanunta "Na shiga Uku ni Suwaiba jikar mai Koko, yaro ƙarami da kafirar zuciya sai ka ce mushrikan farko?"
Sagira ta yi 'yar dariya kana ta ce "Da ma shi ya sa ake so ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru, kuma ka shuka alkhairi domin ka girbi iri mai kyau."
"Me kike nufi 'yar nan?"
"Uhm bakomai Iya ki ba ni goron sauri nake Inno tana jirana a gida."
Daga haka ta miƙa hannu ta karɓi goron a hannun Iya ta fice daga gidan yayin da ta bar Iya a tsaye cikin jimami da kuma neman tarjamar zancen Sagira.
Saurin kauda wannan tunanin ta yi a ranta saboda gulmar da ke ciyo ta.
Ta juya zuwa ɗaki tana ƙwalawa yarta Sakina kira. "Ke Sakina kina Ina ne wai?"
Daga cikin ɗakin Iyar Sakina take faɗar "Iya gani nan a ɗaki."
"Maza ki fito, ki yi sauri ki je ta wajajen gidan Halima ki gano mana meke faruwa." Ta faɗa tana nufar ɗakin.
Cikin zumuɗi Sakina ta fito yafe da mayafinta ƙarami tana faɗar "To Iya me ya faru a can?."
"An ce wai Anas ɗinta ne ya yi kisan kai."
"Kai! Bari na yi sauri Iya wannan rahoton mai zafi ne." Ta faɗa tana nufar ƙofa.
Can bayan wasu mintuna masu tsayi sai gata ta shigo gidan har tana sassarfa. Ta nufi inda Iya ke zaune a cikin daki tana cin abinci tare da kallon TV ta ce "Iya na dawo."
"Yawwa yar albarka zauna ki bani na sha."
Ta matsa kusa da Iya ta zauna tare da jefa hannunta a cikin abincin ta fara kai loma tana faɗar "Ai kuwa Iya ta tabbata satar Hajiya a Makka, zancen nan haka yake."
Ta sake saka loma tana faɗar "Ina fita daga nan ban zame ko'ina ba sai gindin rijiyar da ke kan kwanar gidan Anty Halima koda na ƙarasa ana yunƙurin ɗauke gawar yaron a wurin mutane sai surutai suke yi akan Anas. Na samu wuri na maƙe a cikin yan kallo har sai da kowa ya watse, da na ga iya hakan labarin bai gamshe ni ba sai na nufi gidan Anty Halima don samo cikakken labarin."
Ta kuma auna wata ƙatuwar loma, kafin ta Hadiye ta buɗi baki da nufin ƙarasa labarin, cikin rashin sa'a shinkafar ta sarƙafe mata a maƙoshi, sai ta hau tari da yunƙurin amai.
Cikin azama Iya ta janye kwanon abincin gefe tana faɗar "Sannu sannu karɓi ruwa ki sha." Ta miƙa mata kofin ruwa ta ɗaga ta shanye tas amma har zuwa lokacin tarin bai sake ta ba. Dakyar aka samu ta dawo hayyacinta ta ƙarasa cin abincin. Wannan dalilin ne ya saka bata sake magana ba har ta ƙarasa cin abincin. Za ta miƙe ta fita kenan yayarta Zam'atu ta shigo ɗakin riƙe da ledoji manya-manya guda biyu.
Tuni Iya ta yashe baki tana faɗar "Sannu da zuwa yarinyar kirki me aka samo mana ne?"
Da alamun gajiya a tattare da ita ta karasa kusa da Iyar ta zauna kan kujera tana ture ɗankwalin kanta tare da faɗar "Wash! Na gaji sosai wallahi, bari na je ɗakina na yi wanka. Ta miƙe har ta kai ƙofa ta waiwayo.
Wannan ɗayar ledar kaza ce da sauran tarkace na siya maku, kin san yau na karɓi albashina. Ita kuwa yeluwar leda Sakina ki kawo mini ita ɗakina Yanzun nan kayana ne a ciki."
Tana gama faɗa ta fita ta bar Iya na yashe haƙora da faɗar "ga shi dai mun riga mun ƙoshi yanzu, Sakina saka mana a firij ɗin can an jima sai mu ci."
Da murna Sakina ta miƙe ta aiwatar da umurnin tsohuwar tata, duk da cewa Allah Ya zuba mata tsinannen kwaɗayi amma duk da haka idan ta riga ta ƙoshi ko ɗawisu ka bata ba za ta ci ba.
Zam'atu 'yar yayan Iya ce wanda suke ciki ɗaya tun bayan rasuwar mahaifiyarta riƙonta ya dawo hannu Iya lokacin bata fi shekara goma ba a rayuwa.
Miƙe wa Sakina ta yi ta ta fitar da kwanon waje sannan ta je ta ɗauko ledar yayar tata ta nufi ɗakin.
Tana turawa ƙofar sanyin A.c da daddaɗan ƙamshin turaren da aka buɗaɗa a ɗakin ya daki hancinta, da hanzari ta ƙarasa shigewa tare da rufe ɗakin ta nufi yayarta tana Murmushi ta miƙa mata ledar.
Ɗaki ne ciki da falo, fakon mai matuƙar faɗi ba ta sami yayar a farkon ba sai ta wuce uwar ɗakan da ya kasance ɗan madaidaicin ɗaki da ke ɗauke da banɗaki da gado ɗaya a gefe, gefe ɗaya walldrop ce mai kyau yar madaidaiciya a uwar ɗakan. Ƙasan ɗakin kuwa ya sha tiles mai santsi sai ƙyalli yake har kana iya hango fuskarka a ciki. A gefe ga madubi da kayan shafa.
Duk da ba yi wa ɗakin wani ado mai yawa ba, amma kallo ɗaya za ka yi masa kasan an kashe kuɗi kuma ɗakin na yan gayu ne. Duk a cikin gidan shi kaɗai ne daki mafi ƙayatuwa da ya banbanta da sauran ɗakunan da ke gidan.
Gidan ya kasance gidan gadon Sakina ne da yayanta Saƙibu, tsohon gida ne na magada daga baya ne aka gyara wasu sassa na cikinsa.
Sakina ta zauna tana faɗar yaya "don Allah buɗe na ga meye a ciki na ƙagu fa sosai."
"To uwar azarɓaɓi ai sai ki buɗe tunda kina da hannu."
Da hanzari ta zazzage kayan ciki akan center Capet mai laushi dake malale a ƙasan ɗakin.
Wasu lesuka guda biyu ta gani masu masifar kyau, ɗayan kalar purple ɗaya red sai atamfa guda biyu da wasu turarukan feshi masu ƙamshin gaske.
Koda gani ba sai ta nemi ƙarin bayani ba ta san masu tsada ne sosai. Sun burge ta matuƙa hakan ya sa ta ce "Wow! Gaskiya yaya kayan nan sun yi masifar kyau don Allah in ɗauki wannan?"
Ta ɗauko ɗaya daga cikin turarukan ta nunawa Zam'a.
"Cab lallai ma yarinyar nan! Wannan mai tsada ne sosai na siyo shi ne saboda amfanin kaina, maza ki ajiye shi."
Ta nuna mata wani turaren tana faɗar "Ki ɗauki wannan shi ne dai-dai ke." cike da murna ta ɗauka tana faɗar "Na gode sosai yaya Zam'a gaskiya yaya Alhaji yana ji da ke, ji yadda ya samo miki aiki mai tsoka, har kika samu damar gyara ɗakinki da halaliyarki, Allah dai ya nuna mana auren nan naku ranar za a kantama biki irin wanda ba a taɓa yi ba kaf unguwar nan."
"To na ji, maza ki tashi ki tafi na ɗebo gajiyar wurin aiki ina so na huta ne."
Sum-sum ta miƙe ta fice daga ɗakin tana cuno baki, don duk rashin kunyarta tana tsoron yayar tata don ta fita iya rashin mutunci idan har aka taɓa ta.
****
Bayan kwana biyu Halima ta dawo majalisar tasu inda suka ajiye faifan kasa sirrukan mutane tare da ci gaba da kassafawar kuma suna siyar da asirin ga duk wanda ya so, wani lokacin ma a kyauta suke bada sirrin idan kudinka bai kai ba.
Bayan wani lokaci mai tsayi Iya ta riski kanta cikin tsananin damuwa da nadama da ta wayi gari ta riski Sakina da cikin halin ciwo na typoid. Duk da likitoci sun tabbatar mata da typoid ce amma a tsorace take kada zargin jama'a na cewa ko Sakinar ciki tayo, don wannan kusan shi ne rahoton da yake ta yawo a bakin jama'ar unguwar ba tare da sun tabbatar da takamaimen abin da ya sami Sakinar ba, hujjar su kawai yawan laulayin ciwon nata da rikicewar sa. Haka ta ƙara ɗaukar ta zuwa asibiti na gaba inda aka ƙara tabbatar mata da typoid ɗin ce.
Ga shi kuwa Iya tana tsananin son yar nan tata, ita kaɗai ta rage sanyin idaniyarta tunda shi Saƙibu ya tare a Legos har ya yi aure a can ya ƙi waiwayowa.
Abin duniya duk ya taru ya yi mata yawa, ta rasa gane ya za ta warware matsalar jama'a su fuskanci gaskiyar al'amari su daina aibanta mata 'ya.
Zam'atu ce take ta ba ta baki da lurar da ita cewa ta daina saka damuwar maganganun mutane a ranta tunda har ita ta san gaskiyar lalurar yarta ta. Ana tsaka da haka kwatsam aka wayi gari da gawar Sakina da typoid ɗin ta ci ƙarfinta a tsakiyar dare.
A ranar Iya ta sha kuka har ta ba wa uku lada. Ba ta raba ɗayan biyu zagi da cin naman 'ya'yan wasu da rashin yi masu uzuri ne ya haifar mata da wannan abin.
Ga shi ta rasa yarta tana yawan ji ana cewa idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta ka yi hanzari ka shafawa naka ruwa. Amma ita a maimakon ta shafawa nata ruwa sai ta shafa masa kalanzir kuma ta kunna maƙesci. Ga shi ta rasa gemun gaba ɗaya.
A haka mutane suka ta zuwa yi mata gaisuwa amma duk wanda ya zo sai ya yada mata ƙaramar magana a bisa zargin da suke cewa garin zubar da ɓoyayyen ciki ne ta rasa yar tata.
Yanzun ma haka ta faru, gidan cike yake da jama'a wasu na shiga wasu na fita. Yan layin su Inna Luba (mamansu Hanifa) ne suka zo yi mata gaisuwa.
Inna Luba ta kada baki ta ce "Sannu Iya! Ashe ita kuwa Sakina wannan al'amari haka ya faru?, ashe mai bunu a gindi ne ke kai gudunmuwar gobara. Ba zagin da baki yi wa Yayana ba a nan, ashe wannan ta ɗara su a komai ma."
Zam'atu ce ta hayyaƙo mata cikin masifar da ta manta rabon da ta yi irinta ta ce "Ke Luba! Ki kiyaye hawa kan babban titi yayin da yake cunkushe da ababen hawa, don ba makawa zaki sha murza. Har ke wacece da zaki zo har cikin gidanmu ki zagar mini yar uwa? Ki bar mu mu ji da abin da ya dame mu."
Inna Luba ta yi dariya "Hahaha! Da ma ai zaki aikata tsohuwar mara mutunci irinki wannan ba komai ba ne a gare ta don ta ci zarafin tsofaffi, shi ya sa har yanzu ko auren fari ya gagare ki."
Ai kuwa Zam'a ta yo cikinta kamar za ta kai mata duka matan da ke wurin suka janye ta ɗa kyar, sannan ne aka samu aka fitar da Inna Luba daga gidan. Iya dai ba baki sai kunne ta sani mutane da yawa suna da gyambonta kuma ba makawa za su ci gaba da amfani da wannan damar don su fashe ƙurjinta, ba ta da shaida sai Allah don ko ta nuna musu takardar gwajin jinyar da Sakina ta yi ba yarda za su yi ba. Za ma su iya cewa daga baya ta yo takardar don wanke yarta daga zargi.
A kan tilas ta yi haƙuri da duk wata magana da ake yaɓa mata ta haɗa da ruwa ta taushe. Haƙiƙa ta ga izina.
Tun daga wannan lokacin ta yi ƙoƙarin kiyaye harshenta daga aibata yayan wasu da kuma gulma.
Duk lokacin da ta ji an faɗi mummunar kalma akan matacciyar yarta sai ta zubda hawaye.
A ranta tana cewa 'Kaicon halina, kaicon wannan bakin nawa da ya yi ta aikata ya'yan wasu ba tare da sanin irin raɗaɗin da iyayen su ke ji a ransu ba yayin da kalamaina suka isa kunnuwansu. Ya zama wajibi a gare ni na kiyaye harshena daga yasasshiyar magana da ƙananan maganganu saboda na ga izina.'
UMMU INTEESAR CE
managarciya