WATA UNGUWA: Fita Ta Uku

Miƙewa tsaye ya yi yana Faɗar "Ban ga laifinka ba Ma'eesh har yanzu baka san me ake kira so ba tunda ko budurwa ɗaya baka da. Cire so daga zuciya ba abu ba ne mai sauƙi. Da zan iya a yau da na fizgo soyayyar Mahee daga raina na watsar da ita ko na samu Salama a zuciyata, sai dai abun takaicin har yanzu sonta dake zuciyata bai ko  jijjiga ba bare ya tarwatse. Haƙiƙa wannan jarabawa ce mai girma, kawai ka taya ni da addu'a."

WATA UNGUWA: Fita Ta Uku

WATA UNGUWA: Fita Ta Uku

Free p3

 

BABI NA UKU

 

Wani kyakkyawan saurayi ne durƙushe akan gwuiwoyinsa ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo ya na fuskantar wata 'yar kyakkyawar budurwa cakulet "Don girman Allah Mahee ki taimakawa rayuwata, ban zo nan don na yaudare ki ba,tsananin so da ƙaunarki ne suka mun jagora zuwa gurinki duk da kina wulaƙanta ni, na kasa barinki ki jure ki sama mun matsugunni a zuciyar ki komai ƙanƙantarsa in fake."

 

Wani mugun kallo ta bi shi da shi tare da jan wani siririn tsaki "Gaskiya wannan ganyen ka yada zuciyarka kare ya ɗauka, sau nawa zan gayama ka fita harkata, amma ka ƙi ji?"

 

"Ki dai ƙara haƙuri sahibar zuciyata ina matuƙar ƙaunarki ne shi ya sa..."

 

"Don Allah dakata malam!

Ta faɗa cikin tsawa tare da ɗaga masa hannu. "Irfan kake kowa? Ka saurare ni da kyau, don Allah ka fita harkata domin ina da wanda nake ƙauna, dukiyarka ba ita ce a gabana ba. Ni ba zaka iya siye ni ba kamar yanda ka siye mahaifana, don haka ka je Allah ya haɗa ka da rabon ka....."

 

Har ya bude baki zai sake cewa wani abu, ta ja wani uban tsaki ta wuce fuu abunta ta bar shi nan ɗurkushe a cikin zauren.

Duk da cewa yana tsananin ƙaunarta duk irin cin kashin da take masa baya damuwa amma wannan karon ya ji ciwon abun da ta masa sosai.

Miƙewa tsaye ya yi tare da juyawa ya bar soron gidan zuciyarsa ba daɗi. Tabbas da ba don Maheerah ba ce ko wace yarinya ce ta masa kwatankwacin haka zai bar ta barin mantuwa.

Amma abun mamakin shi ne ko kaɗan bai ji son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Hakika so makaho ne baya iya ganin matsugunnin da ya dace da shi, da ba don haka ba kyakkyawan saurayi kuma ɗan gata me zai yi da Maheerah 'yar talakawa?

Tafiya ya fara yi yana nufar inda ya faka motarsa domin mota bata iya shigowa layin na su, bai yi aune ba sai ji ya yi ya ci karo da mutum. A take ya ji ransa ya ƙara ɓaci.

Cikin hanzari ya ɗago kansa da niyyar ya sauke zafin akan koma waye.

Daidai lokacin ita ma ta ɗago kanta da nufin ta amayar masa da ruwan masifar dake cikinta sai dai me?

Suna haɗa ido ta yi saurin soke kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

‘’ke wace irin jaka ce? Ko ke makauniya ce da zaki hada ƙazamin jikinki da ni’’ ya fada cikin daga murya yayin da yake binta da kallon tsana.

So take ta dago kanta ko don ta ƙare masa zagi, amma ko kaɗan zuciyarta ta kasa amincewa da wannan tunanin nata.

Ganin bata da niyyar magana kuma har yanzu bata kauce daga gabansa ba ya saka shi ratsawa ta gefenta ya wuce ya na faɗar "Ka da ki sake haɗuwarmu ta gaba ta kasance haka domin komai zai iya faruwa.’’

Bayan tafiyarsa Sofi  ta juyo baya tana kallonsa a ranta ta ce "Gaskiya kyakkyawa ne ajin farko, da yana masifar ma sai ya ƙara kyau.’’ Tana zuwa nan a zancen zucinta murmushi ya ƙwace mata.

Tsayawa ta yi tana kallonsa har ya shige motarsa ya bar gun, sai da ta daina hango motar sannan ta bar gun cike da nishadi.

A bangaren Irfan kuwa ko da ya je gida ya tarar da abokinsa Ma'eesh a ƙofar ɗakinsa yana jiran zuwansa.

 

Tun daga yanayin shigowar motarsa cikin gate ɗin Ma'eesh ya fahimci akwai damuwa tattare da abokin nasa, bare yanzu da ya ƙaraso suna gaisawa kallo ɗaya ya masa ya tabbatar da zargin da yake a kansa, Lallai ya na cikin damuwa sosai.

"Sannu da ƙarasowa matumina." Ma'eesh ya faɗa ya na kallon ƙwayar idon Irfan.

 

"Yawwa Abokina, yi haƙuri ka zo bana nan, wallahi na manta da na kira ka akan ka zo, shiyasa ban gayama ba da zan fita." Ya faɗa ba walwala.

 

"Ah! Badamuwa Mutumina ko dai an je gurin Sahibar ne?.." ya faɗa yana yar dariya.

 

A maimakon Irfan ya ba shi amsa kawai sai ya saka maƙulli ya na ƙoƙarin buɗe ƙofar, can ya ɗago yana faɗar "Mu ƙarasa daga ciki." Ba musu ya bi bayan Irfan ɗin suka shige ƙayataccen ɗakin nasa da ya sha ado da kayan alatu, tamkar dai ɗakin wata Amarya.

 

Zaunawa Ma'eesh ya yi yayin da Irfan ya ƙarasa gun firji ya dauko musu ruwa da lemo.

 

"Ko dai gimbiyar ta maka halin nata da ta saba ne?" Ya ji tambayar kamar daga sama.

 

Juyowa ya yi ya na kallon Ma'eesh "Me ka gani ne?"

 

"Na ga damuwa tattare da kai wanda ba haka kake ba kafin awa biyu baya da muka yi waya da kai." Ya maido masa amsa.

 

Zaunawa ya yi zugudum bai ce komai ba, Ma'eesh ya matso kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa yana faɗar "Ka ga Abokina wannan yarinyar fa bata ƙaunarka rabuwa da ita shi ne kawai zai sama maka salama a zuciyarka."

 

Ajiyar numfashi Irfan ya sauke bai ce komai ba, sai Ma'eesh ne ya sake magana a karo na biyu. "Irfan ina mai ƙara gayama ka cire wannan yarinyar a ranka, ga tarin 'yanmata nan da yawa a gari? Ni na rasa me ka gani a jikin wannan busasshiyar 'yar talakawar duk da tarin ƴaƴan masu hannu da shuni dake ƙaunarka, amma ka maƙale sai ita, Sam ita ba ajinka ba ce Irfan."

 

Miƙewa tsaye ya yi yana Faɗar "Ban ga laifinka ba Ma'eesh har yanzu baka san me ake kira so ba tunda ko budurwa ɗaya baka da. Cire so daga zuciya ba abu ba ne mai sauƙi. Da zan iya a yau da na fizgo soyayyar Mahee daga raina na watsar da ita ko na samu Salama a zuciyata, sai dai abun takaicin har yanzu sonta dake zuciyata bai ko  jijjiga ba bare ya tarwatse. Haƙiƙa wannan jarabawa ce mai girma, kawai ka taya ni da addu'a."

 

Girgiza kai kawai Ma'eesh ya yi yana jinjina girman soyayyar Irfan ga Mahee.

 

Ita kuwa Mahee tana shiga gidan ta wuce ɗakinta cike da takaicin na ci irin na wannan mutumin. Tsaki ta ja tana faɗar "Mutum sai ka ce jikan Mayu? Ni na tsani naci  a rayuwata wallahi."

 

Can ta lalibo ƙaramar wayarta tana yunƙurin kiran abun ƙaunarta Ja'afar. Kamar daga Sama Umma ta faɗo ɗakin tare da fige wayar a hannun Mahee tana faɗar "Sannunki da zubar mana da ƙima, wai ke meke damun ƙwaƙwalwarki ne? Ga Arziƙi ya na kiran ki kin toshe kunne, to wallahi bari in gaya miki tun wuri ki sake shawara kafin abun ya isa kunnen mahaifinki."

 

Turo baki ta yi tana faɗar "Ni dai gaskiya bana sonsa Ja'afar kawai zan aura, shi arziƙi ai nufin Allah ne."

 

Bige mata baki Umman ta yi sai da ya fashe ta ce "To marar kunya, ana nuna miki Annabi ki na runtse ido, wannan lalataccen yaron kike so mu aura miki, bayan ga nagartacce ɗan gidan manya?"

 

"Ni dai shi nake so, da shi kaɗai na ji zan iya rayuwa, aba ni shi ko in....." Ta faɗa yayin da ta miƙe ta bar ɗakin.

 

"Iyyeah! Lallai yarinyar nan abun naki azimun ne, bari malam ya dawo gidan..."

 

Da misalin ƙarfe tara na dare Ja'afar ya shirya tsaf cikin ƙananun kayansa ya nufo gidansu Maheerah.

 

Malam isah na kwance ƙofar gida ya na tsaye ƙofar gida shi da baƙonsa kawai Ja'afar ya zo ya wuce su zuwa cikin Soron gidan ba ko gaisuwa sai bubbuɗawa yake.

 

Malam Hadi dake tsaye tare da Malam Isah ya kama haɓa tare da faɗar "Yau na ga abinda ya fi zare tsawo. Anyah! wannan yaron da ƙwaƙwalwa a kansa kuwa? Taya zaka zo ka wuce mai gida bako Sannu."

 

"Gane mun hanya dai malam hadi... Am! Ina zuwa bari na je na ji da wacce ya zo."

 

Yana gama faɗa ya bi bayan Ja'afar zuwa cikin Soron...

 

Shigarsa ya yi dai-dai da shigowar Maheerah soron tana cewa "Kai! gayena ka ga yanda ka wanku kuwa?, yasin kamar na haɗiye ka." Wata shu'umar dariya ya yi.

 

Jin hakan ya dasƙarar da Malam Isah gurin, ganin Ja'afar ya matsa ya na neman bata hannu su gaisa ya dawo da shi daga duniyar mamaki "Ke mutuniyar kawai!"

 

A tsorace ta ɗago jin Muryar mahaifinta, idanunta suka sauka kan fuskar dattijon mai farin gemu. Fuskarsa a murtuƙe take ba annuri, ta yi saurin gano haka ne saboda wadataccen hasken gwalaf ɗin lantarkin da ya mamaye ilahirin soron.

 

Nan take antar cikinta ta kaɗa.

 

"Za ki shiga ciki ne ko sai na tattakaki?" Ya kuma faɗa cikin ɗaga murya.

 

Ai bata san lokacin da ta shige cikin gidan da gudu ba tsabar tsoron da take ciki.

 

Juyowa ya yi ya na fuskantar saurayin "Kai kuma na dawo gare ka, waye ya baka izinin shigo mun cikin gida, kuma waye kai?"

 

"Amsar tambayarka ta farko yarka zaka tambaya ba ni ba. Amsa ta biyu kuwa ni ɗan ƙwalisa ne wanda mata suke nacin so, ko ban zo ba za'a je mun Jafsee guy kenan."

 

Ya ƙarasa zancen ya na shu'umin murmushi tare da gyara kwalar rigarsa.

 

'Inda ranka ka sha kallo.' Malam isah ya faɗa a ransa yana ƙarewa yaron kallo.

 

Ko kaɗan shigarsa bata yi kama da ta ƴaƴan hausawa ba, shi kallon arne-arne ma yake yiwa yaron duba da irin sunansa da ya faɗa, ga wani uban gashi da ya tara duk ya mummurɗe tamkar hauka sabon kamu, sanye yake da wani ɗamammen wando irin wanda gayu suke kira (crazy).

 

"Ba shakka yaro ka cika marar ta ido, amma dai ba a nan unguwar kake ba ko?"

 

"Ka faɗi dai-dai mai farin gemu, ban da albarkacin kyakkyawar 'yarka wato Babyna ban ga abinda zai shigo da ni wannan ƙazamar unguwar ba. Na san ba zaka rasa sanin Unguwar Dagarma ba, (rigima ga mai ƙare ki idan a tafe kake to mu a hanya muka kwana, Dagarmawa kowa ya tara ya samu.) Kirarinmu kenan." Ya faɗa.

 

"Yaro fice mun daga gida, daga yau bana son sake ganinka a nan gidan, ita ma wace ta janyo kan zan yi maganinta ne.

 

Malam Isah ya faɗa cikin zafin rai.

 

"Kwantar da hankali Malam yanzu kuwa zan bar maka kangon da kake kira a matsayin gida." A yanda ya yi maganar sai ka rantse ɗan gidan wani hamshaƙi ne nan kuwa gidan da ya kira da kango ya fi nasu tunda har ya samu albarkacin ginin bulo, na su kuwa yunɓu ne.

 

Ficewa ya yi daga gidan.

 

Shi kuwa Malam isa ya shige cikin gidan tuni ya manta da wani baƙo da ya bari a waje tsabar ɓacin rai.

 

"Indo! Indo!! Ke Indo!!!

 

Umma ce ta fito da sauri har tana tuntuɓe saboda jin wannan gigitaccen kiran.

 

"Ga ni Malam lafiya?"

 

"Tambayata ma kike? Ki na aikin me Maheerah ta janyo mun wannan lalataccen zuwa gidana? da ƙimata da komai tana neman zubar mun da mutunci." Ya faɗa ya na huci.

 

"Yi haƙuri Malam wallahi ban san lokacin da ta fice daga gidan nan ba." Ta faɗa cikin tsoro.

 

Haƙiƙa ta firgita ainun da ganin yanayin mijin nata.

 

"Tana ina Maheerar?" Ya faɗa da ƙarfi.

 

Maheerah dake ɗakinta kwance cikin tsoro jiyo Muryar Mahaifin nata yana nemanta ya ƙara sakawa ta tsinke. Takurewa ta yi guri ɗaya tana jiran sakamako.

 

Ita bata san da dawowarsa ba da ko giyar wake ta sha ba zata kira Ja'afar zuwa gida ba, saboda gudun hakan.

 

Ɗakin ya shigo ba ko sallama hannunsa riƙe da wata tsabgegiyar carbi da yake ja.

 

"Ke waya baki izinin gayyato mun wannan mara tarbiyyar zuwa gidana?"

 

Shiru ta yi kamar ruwa ya ci ta.

 

"Waye shi a gare ki?" Cikin rawar murya da tsoro ta ce "Saurayina ne Baba." Ta san abunda kalmar zata iya janyo mata amma ta kasa jure rashin furtata, ta yanke a ranta in dai akan Ja'afar ne sai dai a kashe ta ba za ta sauya ra'ayi ba."

 

"Lallai wuyanki ya isa yanka, ni kike gayawa haka bayan kinsan na hanaki kula kowa in ba Irfan ba?"

 

"Baba bana son Irfan, wallahi na tsane shi ni Ja'afar kawai nake so."

 

"Waye Ja'afar kuma?" Ya tambaya cikin takaici da mamaki, shi a tunaninsa 'yarsa ba zata taɓa samun saurayi kamar Irfan ba wanda ya haɗa komai na nagarta ga kuma kuɗi, duk da cewa shi ba sune a gabansa ba kyawawan halayensa yake so.

 

"Shi ne ya zo yanzu." Ta mayar mai.

 

Ai ji ya yi kamar ta daka masa wuƙa a kahon zuci, nan da nan zuciyarsa ta rufe ya yi kanta gadan-gadan carbin dake hannunsa ya shiga tsula mata iya ƙarfinsa sai ihu take. Can carbin ya tsinke ganin bai gama fanshe haushinsa ba ya rarumo wani ice dake rabe a bangon ɗakin ta waje ya yi kanta ba ji ba gani........