DUHU DA HASKE: Fita Ta Takwas
DUHU DA HASKE:
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 8*
~Washe gari ya shirya tsaf cikin farin riga me showing sannan yasa wando fari yayi kyau sosai, gashinshi ya taje tareda gyara sajenshi yayi kyau sosai, jakan da yake sa takaddun ya ɗauka sannan ya rataya a bayanshi ya zagayo dashi ta gabanshi yasa earpiece a kunne sannan ya fita, yau meesha batazo ba yasan ba lafiya ba, gidansu yaje da sallama ya shiga, yace "Anty ina meesha?"
tace "wallahi ciwon ciki ta kwana dashi tun jiya"
da sauri ya shiga ɗakinta tana kwance akan gado tayi shirin zuwa su tafi aiki amma ciwon cikin yaci karfinta, yace "sorry ko na kira hamisu me chemist?"
girgiza kai tayi tana ciza baki tace "na saba da ciwon cikin kaima ka sani nan da kwana biyu zai daina"
yace "sorry"
jijjiga kai tayi tace "zaka je yau kai kaɗai?"
girgiza kai yayi yace "sai kinyi sauki zamu je"
girgiza kai tayi ta tashi da kyar ta zauna tace "dan Allah kaje watakila idan muna tare bakada sa'an samun aiki may be yau ka dace"
shafa fuskanta yayi yana murmushi yace "ke ko? idan kinyi magana kamar wata babba"
murmushi tayi itama tace "tashi kaje kada kayi late"
ya make kafaɗa yace "no nidai ina kusa dake sai kinyi sauki"
ɓata rai tayi kamar bata taɓa dariya ba tace "shikenan"
ganin ranta ya ɓaci yace "kiyi hakuri zan tafi"
sakin fuska tayi tace "yawwa ko kaifa"
yace "to kimin addu'a"
a hankali ta rike kanshi tana mishi addu'a saida ta gama tace "Allah ya kareka da kariyansa ya baka abinda zaka je nema"
murmushi yayi yace "thank you princess"
tafiya yayi fahad yace "yawwa ya Abdul ka kaini school yau tunda unty Ameesha batada lafiya"
yace "muje"
akan mashin nata suka tafi ya kai fahad school kafin a juya ya tafi, tuki yake yana jin waƙa yana kaɗa kanshi sam baya jin daɗin tafiya babu Ameesha ya saba duk inda zaije tare suke zuwa, yana zuwa company ɗin ya shiga har ciki da mashin kai tsaye babu wani tsoro, kowa sai kallonshi yake, parking yayi ya sauko ya shiga ciki rataye da jakan, zama yayi a inda yaga suna zama da alama yau ta rigashi zuwa domin har an fara interview, manal tana zaune akan kujera ta cika tayi fam sai huci take kamar zata fashe, tunda ta fara yau kwana uku kenan babu ƙwararren data samu abin ya rinƙa cimata rai, tana kallonshi har layi yazo kanshi, knocking yayi da mamakinshi yaji tace "yes"
a takaice kawai, yana shiga kafin tace ya zauna ya zauna a kujeran dake gabanshi yana facing nata, cikin zafin rai tace "tashi"
tashi yayi ya harɗe hannu a kirji yana kallonta, rai a ɓace tace "sauke hanu kasa"
sauke hanun yayi tace "cire earpiece na kunnenka"
cirewa yayi, tace "naga takaddunka"
bata takaddun yayi, ta fizge tana hararanshi ta fara dubawa, ajewa tayi tace "suna"
yace "akwai akan takaddan"
cikin ɓacin rai tace "na gani kuma na tambaya"
yace "ABDULRAHMAN HARUNA LAMIƊO amma anfi sanina da Abdul best friend ɗita kuma ameesha tana kirana da Man"
tsaki taja tace "tace meka sani akan zane?"
yace "abinda baki sani ba na sani akan zane domin tun ina yaro nake zane"
wani irin mugun kallo ta aika mishi, fuskanta kamar an aika mata sakon mutuwa tace "kasan ni wacece?"
yace "manal unar maidawa c.e.o ɗin companyn m.u.m fashion designing ƙwararriya wajen zane wacce ta samu award biyar ciki harda best designer of the year guda biyu, wacce ta karɓi kwangilan zanen hotuna dubu biyar daga wajen manyan ƴan kasuwan zane na kasar nan, tana so ta bunkasa company ɗinta ta yadda zata fara harka da manyan masu zane na duniya...."
a tsawace tace "ya isa"
shiru yayi bai kara cewa komai ba sai kallonta da yake, shi bai taɓa ganin mace me masifa da karfin zuciya kamar wannan ba, tashi tayi tana kallonshi tura mishi plain paper tayi a gabanshi sannan tazo dab inda yake ta tsaya tana zane, gani yayi ta zana budurwa tayi fentin rigan red da pink tace "inaso ka fitarmin da sauran color ɗin da zai ƙayata wannan hoton idan har ka kware a zane"
hanunta tasa akan table ɗin duka biyu ta ɗan rankwafa tana kallonshi, murmushi yayi ya ɗau zanen yana kallo, nuna mata yayi yace "tun farko kin ɓata color tunda kika haɗa red color da kuma pink color, red da pink kaloli ne masu zaman kansu suna buƙatan wasu kaloline dokin suyi kyau, dab ita ya tsaya yana kallon cikin kwayan idonta ya yaga takaddan ya zubar a kasa, ya janyo plain paper ya ɗauko kala ya fara zane, kallonshi kawai take har saida ya gama taga ya ɗauko kala red da baƙi ya juyo da hoton yadda zata gani, da mugun mamaki take kallon hoton ganin itace ya zana a yadda take tsaye ta ɗaura hanu akan table ɗin, yace "bakya gani da kyau ne kayan jikinki red ne da baƙi, shi red yafi kyau da baƙi ko kuma fari"
kallon hoton take ko ita ba zata iya zana wannan hoton ba, ganin yadda take mamaki yace "kin gane?"
fizge takaddan tayi ta ɗau takaddunshi badan taso ba saidan tana so ta bunkasa company ɗinta ranta yana tafasa tace "an ɗaukeka aiki ran monday zaka fara zuwa albashi 300k"
murmushi yayi sannan ya rataya jakanshi ya maida earpiece ɗin yace "thanks"
fita zaiyi ta ɗaga murya tace "dokokin company"
cak ya tsaya ranta yana tafasa tana magana tace "duk ranan dana shigo naga na rigaka zuwa na koreka a aiki, ina zuwa waje zaka tashi banson kowa ya zauna ina tsaye har sai na zauna, babu dariya babu wasa domin aiki akazo ba wasa ba, babu taɓa abinda yake mallakina ne kamar frij ɗina da sauran abubuwana iya kacinka aiki"
yace "deal"
fita yayi daga office ɗin ta dunkule hanu ta buga da kujeran gabanta cikin baƙin ciki tace "banso wannan ne ya zama me taimakamin a zane ba, amma ba komai i will deal with him"
yana fita ya hau mashin ɗin cikin zumuɗin zuwa faɗawa ameesha ya tafi gidansu, gani yayi a kulle, da sauri ya kira Imran yace "ina Ameesha?"
Imran yace "gamu nan tare dasu umma fahad ya dawo wai baida lafiya amma yanzu yayi sauki"
yace "okay"
kashe wayan yayi ya wuce direct gidansu, yana zuwa ya shigar da mashin ɗin ciki, a hankali yake tafiya kamar marar lafiya, Ameesha dake zaune a kasa umma tana kitsa mata kanta guda biyu taga ya shigo jiki a mace, shiru tayi umma ta gama mata kitson, tashi tayi kitson ya sauko har bayanta zuwa hips nata dake cikin wandon jinx, riga me kamar vest ne a jikinta tayi kyau sosai, Anty tana zaune a gefe fahad ya kwantar da kanshi a cinyarta yana kallon man ɗin, Imran dake zaune kusa dasu yace "yauma an kuma"
murmushi tayi mishi kana ta rike hanunshi cikin san kara mishi karfin gwiwa tace "ka dawo?"
a hankali ya gyaɗa kai, tace "kada ka damu a kullum ina faɗa maka kada kayi giveup nima yau na samu karamin aiki zasu rinƙa biyana 15k a wata, wani company karami a kusa da bakin kasuwa kampanin shinkafa ne zan zama musu me rubuce rubuce harma sun bani laptop da zan riƙa zuwa aiki a wajen, ina ganin 15k zai isa mu kara akan kuɗin da muke ɗan samu, dashi zanje na karɓo maka motarka data lalace karka damu kaji yauma sun bani 5k gashi sai muje mu ɗauko motar ka ba?"
a hankali ya janyota jikinshi ya rungumeta tsam, shiru tayi tana jinshi yana shafa bayanta, umma ta ɗauke kai tana share hawayen daya zubo mata, Ameesha da man sunsha wahala kuma suna kan sha, Ameesha itace mace ta farko data dage akan rayuwarsu har shi man ta bar karatu sabida ya samu ya kara gaba da secondary akan mashin nata take kaishi school har ya gama, itace take zuwa ta kaishi ta kai su Imran sannan ta ɗaukosu daga school, a hankali yace "meesha?"
idonta cike da hawaye tace "na'am"
yace "kin san me?"
girgiza kai tayi, cikin ihu da jin daɗi yace "na samu aikiiiiiiii"
zameshi tayi daga jikinta tana kallonshi tace "what?"
gyaɗa mata kai yayi yace "na samu aiki"
girgiza kai sukayi su duka sukace bamu yadda ba, wayarshi ya buɗe yasa musu voice ɗin da yayi recording duk abinda sukayi harda albashi 300k
wani irin tsalle Ameesha tayi ta faɗa jikinshi, ɗagata yayi sama yana juyi da ita, umma tazo ta rungumeshi, Anty ma wacce take hawayen farin ciki ta rungumeshi duka dasu Imran suka rungume juna, Ameesha ta zame taje ta ɗauko babban tape ɗin ɗakinsu ta kunna waƙa tana rike da tape ɗin ta fara rawa, suma rawa suka fara tana hawaye tana rawa duk suna biye mata, man ya tsaya kawai yana kallonta ji yayi kamar ya haɗiyeta, a ranan sun yini cikin farin ciki sun manta da duk wani damuwan da suke dashi a duniya, Ameesha dashi sukaje suka ɗauko motarshi dake wajen gyara shi yake driving tana ta farin ciki har suka dawo gida, motan ba wani kyau bane dashi amma dai na laifi, mashin nata ta aje a bayan gidansu ta rufe da tampol tace "bye bye mashin ba zan kara hawanka ba na gode da taimakon da kayi min a rayuwa"
man yana rike da hanunta yace "kimin wani alkwari"
tace "to na me?"
yace "kimin alkawari ba zaki kara hawan mashin ba nine zan kaiki duk inda zakije dan dama hakuri kawai nakeyi idan na ganki akan mashin kina yin kyau sosai kuma hankalin mutane yana kanki"
murmushi tayi tace "amma idan wani uzuri ya kama ni kuma baka nan fa?"
yace "duk inda nake kome nakeyi ki kirani zan bari"
tace "to nayi alkawari"
manal tana shiga gida tana waya tace "yes ranan monday zamu fara kwantar da hankalinku manal ba zataci kuɗin kowa ba"
da sauri tace "two minutes"
kashe wayan tayi ta waro manyan idanunta tace "Ammiiii"
ammi sai murƙususu take a kasa tana juyi tana ciza leɓe, ta fita a hayyacinta fuskanta yayi jajur ta ɓata inda take kwance da jini, da gudu ta wurgar da wayan tazo tana tiketa, damke hanunta tayi tace "manal cikina zan mutu"
bleeding take sosai, gani tayi idon ammi ya kafe a sama, ihu tayi tace "ammii"
sai yanzu ta tuna abinda dr ya faɗa mata akan maganin sai tasha sau uku cikin zai sauƙa, yau ne kuma ta zuba mata na karshen a juice kafin ta tafi, dafa kirji tayi da sauri ta ɗauketa daga wajen, fita tayi daga ɗakin tana cewa "driver!!! driver!!! gateman ka buɗe gate"
cikin ɗingishi yazo wajensu yana cewa "meya samu Hajiya?"
a tsawace tace "ka buɗe gate nace"
buɗe gate yayi driver yazo da gudu ya shiga motan data sa ammi, ta ɗaura kan ammi a cinyarta tana cewa "ammi ki buɗe ido, ki kalleni ammi nice manal"
tace "ka kara gudu"
gudu yake dasu akan titin har suka isa city hospital, ɗagata tayi da gudu babu takalmi ta shiga ciki da ita, wata nurse ta tare kofan emergency tace "da mutum a ciki saide kiyi haku....."
kafin ta karasa manal tasa mata kafa tayi wurgi da ita cikin zafin nama, ji kake tim ta faɗi kasa, jajayen idanunta ta kalleta dasu tace "stay away"
da kafa ta bankaɗa kofar ta shiga da ammi, kwantar da ita tayi akan gado inda ake yiwa wani aiki, da sauri likitocin sukace "ke waya baki ikon shigowa?"
almakaci ta ɗauka tasa a wuyanta tace "idan baku bar aikin da kukeyi kuka dubata ba wallahi saina yanka kaina kuma kunsan sai an rufe wannan asibitin"
da sauri sukace "kada kiyi haka zamu dubata"
dubata suka fara da sauri tana rike da almakacin har suka gama suka ɗaurata akan gado suka fita da ita, tana biye dasu har zuwa wani ɗaki da babu kowa a ciki, akan gado aka kwantar da ita sukace sai an nemi jini, hanunta ta mika musu tace "ku ɗiba nawa"
Dr yace "sai mun gwada kuma Bama...."
almakacin ta nuna mishi a haukace, yace "to to.."
ɗiba jininta yayi tana tsaye tana kallonshi harya gama ta runtse ido da zai cire alluran, saida ya gwada jinin kafin yazo ya sawa ammi, tana kwance idonta a rufe, ta rame sosai ta kara yin fara, ta zubda jini da yawa, manal tana zaune kusa da ita tana rike da hanunta mara jinin tana girgiza kafa, idanunta sunyi jajur, saida jini ya kare kafin ammi ta buɗe ido, da sauri manal tace "ammi kin tashi? Dr!!! Dr!!!!"
da sauri suka shigo suna dubata, ammi ta rike hanunta tace "cikina yana nan lafiya?"
shiru tayi tana kallonta, a hankali dr yace "am sorry to say cikinki ya zube"
fizgewa tayi zata sauka manal ta riketa, kuka ta fara tana cewa "wayyo ɗana wayyoo ɗana, manal ki taimakeni shine kaɗai abinda ya rage da zan gani na tuna umar"
ran manal ya fara tafasa jin tace shine kaɗai to ita ɗin fa? ganin zata fizge tace "ya isa"
a tsawace tayi maganan, ba ammi kaɗai ba harda dr saida ya tsorata, tace "ki koma ki kwanta"
komawa tayi cikin tsoro ta kwanta, ta kalli Dr tace "out"
fita yayi ta tashi tana safa da marwa tana dunƙule hanu, wato data haifi cikin zata daina sona ta fara son cikin?"
cikin ɓacin rai tace "ammi kece kika haifeni?"
a firgice ta kalleta tace "manal wani irin tambaya kike?"
tace "kince wannan cikin ne kaɗai abinda ya rage da zaki gani ki tuna dady ni kuma fa?"
da sauri tace "wallahi manal nice na haifeki meyasa kike yiwa amminki wannan tambayan?"
cikin yadda da ita tace "to idan har bakya so nayi zargi ki manta da wannan cikin daya zube ki ɗau ƙaddara ki rike hannu bibbiyu"
da sauri ta share hawaye tace "na daina insha Allah ba zan kara magananshi ba kinji?"
murmushi tayi sannan ta share hawaye tazo ta zauna a gefenta ta ɗaura kanta a cinyarta tace "kiyi hakuri ammi da tsawan da nake miki ni kaina bana iya control na fushi na?"
girgiza kai ammi tayi tace "ba komai manal"
a ranta tace "ni kuma haka ƙaddara ta take haka Allah ya kaddaramin ba zan taɓa haihuwa ba, Allah na gode maka kuma na karɓa hanu biyu"
shiru suka zauna a wajen babu wanda ya kara magana, tun ran juma'a sai ranan lahadi aka sallamesu da yamma, ta biya makudan kuɗaɗe wa likitocin kafin taja ammi suka tafi gida.
Ameesha goge kayan man take yi tun ɗazu idan ta goge saita kara warwarewa tayi sabon style, umma tace "waini Ameesha baki gajiya ne?"
tana dariya kamar yadda ta saba koda yaushe tace "bana gajiya so nake yayi kyau sosai domin gobe ne first day da zai fara zuwa aiki"
murmushi kawai umma tayi dan koda tace ta daina ba dainawa zatayi ba, tana cikin gugan man ya shigo yana kallonta yace "wai ba kinyi 3hours kina goge rigannan ba meesha?"
tace "Yes so fo*king what?"
girgiza kai yayi, taci gaba da gugan tana faɗa mishi yadda zaiyi idan yaje aikin, ya zuba mata ido kawai a hankali taji yace "i love you"
tana cigaba da guga tace "love you too"
wannan kalman sun saba faɗawa juna ba sabon abu bane a wajensu, har ta gama gugan yana wajen, shiya rakata gida yasan da sassafe itace zata tasheshi daga bacci yace "dan Allah meesha gobe ki ɗan barni nayi bacci tunda an samu aikin"
murmushin tayi sannan ta haɗe rai tace "to idan ka fara late aka koreka ya zakayi?"
yace "please"
shiga gida tayi bata bashi amsa ba.
washe gari kamar ya sani bubbuga kofan take tana kiran sunanshi tashi yayi ya shirya kawai ya fito, umma tace "na gaji da buɗewa Ameesha kofa ta dawo gidan kawai da zama sai nafi jin sauki"
yana buɗe kofan ya ganta tsaye tana murmushi tace "kayi kyau"
ɓata rai yayi yace "thanks"
tace "saide gashinka"
hanu tasa ta gyara mishi gashin tace "good boy"
jerawa sukayi a motarshi suka tafi, ya fara da kaita wajen aikinta ganin wajen yayi mutane dayawa da alama dai wahala kawai zata sha, yace "amma my meesha kina ganin nan babu matsala? tunda na samu aiki kawai ki bari"
buɗe motan tayi tana ɗaukan laptop nata tace "no bazan iya ba, kasan dole kuɗin aikin zai rage mana wani abin kaide kawai idan an tashi zanje na jiraka saimu koma gida tare tunda minti ishirin ne bambancin lokacin tashin mu"
yace "to"
fita tayi tana ɗaga mishi hanu tare da murmushi kamar yadda ta saba tace "bye"
murmushi yayi mata shima yana ji inama ace wajen aikinsu ɗaya, juyawa tayi tana dafa kirji tareda runtse ido ta fara tafiyanta kamar yarinya tana cewa "wayyo wannan katon wajen aikin Allah yasa bai fito ba dan naga ya samin ido"
tana shiga suka haɗa ido, kato ne sosai yana zaune akan kujera yana hararanta, yamutsa fuska tayi sannan tayi kalan tausayi taje ta rike kunne alaman ayi hakuri ta zauna domin tayi late sosai, cikin shaƙaƙƙen muryanshi yace "dama nasan zakiyi late ai shashasha"
a ranta tace "kaima shashasha"
tareda murguɗa baki, yace "me kikace?"
tace "nace ayi hakuri"
rubuce rubucen abinda aka siyar da wanda ya shigo ta fara da duk wani me siya saita rubuta sunanshi da abinda ya siya da kuɗin duka a laptop, wayarta yayi kara tana ɗagawa tayi kasa da murya ta yadda katon ba zai ganta ba tace "hello man ya akayi?"
yace "na shigo gani zaune a office"
tace "nima na fara aiki Allah bada sa'a"
yace "bye I love you"
carap ya faɗa kunnen manal wacce ta shigo tun ɗazu take tsaye tana kallonshi ganin kowa ya tashi shi yana zaune, bai kula ba ya aje wayan yana buɗe laptop nashi, a hankali ya fara waƙa "kece sarauniyaa na baki zuciyaaa kece guda ɗaya...." ɗago kai yayi ganin hall ɗin yayi shiru sosai, waro ido yayi ganin tana tsaye ta gama cika tana huci, waɗannan idanunta me tsoratar da mutane ta zuba mishi, da sauri ya tashi yace "good morning madam"
bata amsa ba kawai ta wuce, hararan bayanta yayi ya zauna a kujeranshi da aka rubuta sunanshi da manyan harufa ABDULRAHMAN HARUNA LAMIƊO
tana shiga tasa a kirashi, zuwa yayi a nitse ya zauna akan kujeran tayi shiru ta zuba mishi ido, ganin tayi shiru shima yayi shiru, tashi tayi ta fita ta barshi batayi magana ba, ganin ta fita ya janyo kulan dake gabanta wanda ammi ta zuba mata indomie cokali yasa ya fara ci dan yunwa yake ji baiyi breakfast ba Ameesha tazo ta kirashi, turo kofan tayi ta tsaya turus tana kallonshi, ji tayi zuciyanta yana tafasa a fusace taje ta kwace kulan tayi wurgi dashi, nan take abincin ya zube, a zafafe tace "waye kai?"
tashi yayi yana kokarin haɗiye abincin bakinshi yace "ni Abdul ne kawai amma kin san babu kyau zubar da abinci haramun ne....?"
tace "kamin shiru"
tana magana jikinta yana rawa tsaban ɓacin rai, tace "tun farkon shigowana ka aikata laifi, aiki kazo ko soyayya?"
yace "bafa so...."
"shout up"
ta faɗa tana kallon cikin idonshi da idonta da suka koma jajur, abincin ta nuna mishi tace "kwashe"
babu musu ya durkusa ya kwashe, tace "get out"
fita yayi, faɗawa tayi kan kujeran kamar tayi ihu dan haushi, iya aikinshi yasa ba zata koreshi ba da yau zai bar company ɗinnan, komawa yayi wajen zamanshi ya fara aikin daya kawoshi, jim kaɗan ta fito fuska babu walwala duk suka tashi harda shi, tace "ku zauna"
zama sukayi tace "yau zamu fara aiki zan bawa kowa plain shit goma goma inaso ku nuna kwarewanku domin gobe zamu tura, nasan akwai zane dubu biyar a rana amma ku daure"
duk suka amsa da "to madam"
mika musu tayi ta basu duk wani kalan da zasu buƙata, itama ta ɗibi plain guda ishirin ta aje a ganbanta ta zauna a kujera ta fara zane, tsit kake ji babu wanda yake magana, man ne yayi atishawa kowa ya kalleshi ɗauke kai yayi yaci gaba da zanenshi, kara atishawa yayi manal bata kalleshi ba tace "fita kaje abaka magani na baka 2mins"
tashi yayi da sauri ya fita, ɓuya yayi yana amsa kiran Ameesha dama shiyasa yake atishawan, ɗagowa manal tayi zata ɗauki kala ta ganshi yana waya yana dariya, shiru tayi harya gama ya shigo, hamdala yayi da yaga bata kallonshi zai zauna tace "bani wayarka"
a hankali ya cire a aljihu ya mika mata, bata kalleshi ba ta karɓa ta aje a gabanta, taɓe baki yayi ya zauna yana aikinshi, da mamakinta taga ya ɗibo plain shit guda ishirin bayan ya gama zana goma data bashi, haɗa ido sukayi yayi mata signal ya saba yiwa Ameesha haka shiyasa, ɗauke kai tayi tana cigaba da zane, kara ɗibowa yayi yana zane, cikin kankanin lokaci ya gama duk paper dake wajen, karɓan na sauran yayi yana zanawa, manal ido ta zuba mishi daya juyo saita ɗauke kai, da haka har ya gama yazo wajenta, tayi kamar bata ganshi ba, gani tayi yaja kujera ya zauna kusa da ita yace "kawo sauran"
kafin tayi magana ya fara zanawa kallonshi kawai tayi, saida ya gama na gabanta ya kalli na hanunta karɓewa yayi ya zana, tafa hanu yayi yace "ko ko ko inji yara zane ya kare ko yau za'a iya tura musu"
fuska ba dariya ta kwashe ta fita dasu, ɗaukan wayarshi yayi, tana fita ta kara kallon takaddun taga zanen da yayi ita kanta saida ta raina zanenta, murmushi akan fuskanta wanda ta jima batayi ba ta wuce wajen mota tasa driver ya kai sakon, jim kaɗan bayan ta koma office aka kirata, godiya suka fara yimata tare da cewa "munji daɗin wannan alkawari da kika cika mun bawa manager ɗinmu dake ƙasar china number ɗinki zaku fara aiki tare"
tsalle tayi cikin jin daɗi tace "think you"
aje wayan tayi tace "god abinda na jima ina nema yau gashi na samu"
shiru tayi yanayinta ya canja tace "sabida wa hakan ya faru?"
a fili tace "sabida wannan useless yaron?"
shiru tayi da alama bataji daɗi ba, Ameesha zuwa tayi ta zauna a bakin kofa tana jiranshi, duk da akwai rana amma baya damunta sosai tana dai jiranshi, ana tashi ya fito da sauri yana ganinta yace "meeshaaaaaa"
da gudu tazo ta murmushi tace "kun tashi? ya aikin da daɗi?"
suna tafiya yace "yes da daɗi kefa ya naki?"
kwaɓa face tayi tace "wancan lukutin ya samin ido"
yace "kin san me?"
girgiza kai tayi, yace "idan nayi wata ɗaya anan ki kawo takaddunki ki nemi aiki saimu dara aiki waje ɗaya"
dariya tayi tace "yeeees"
hanu ya mika mata yace "high five"
zata tafa yaga ta tsaya cak tana kallon bayanshi, juyawa yayi dan ganin me take kallo manal ce take tafiya kamar hawainiya fuska a ɗaure tana aika musu wani kallo, hanun Ameesha ya rike ya tafa yace "pam"
murmushi tayi kanta kasa, saida tasa space nata kafin ta shiga motan tabar wajen da mugun speed kamar zata bigesu, damke hanunshi Ameesha tayi saida taga ta tafi kafin ta buɗe ido a tsorace tace "man ina tsoron wannan boss ɗin"
murmushi yayi yana jan hanunta har wajen mota ya buɗe mata ta shiga gaba ya zagaya yazo ya zauna a mazaunin driver, yace "kar kiji tsoronta idan ta kalleki ki kalleta idan ta harareki ki harareta tanada wuyan sha'ani sosai"
a hankali tace "bazan iya ba"
tsaki yaja suna tafiya yana bata labari, gani yayi tayi shiru ta zama wani kala kuma ya lura tunda taga manal ta shiga wannan yanayin"
yace "meesha"
a hankali tace "na'am"
yace "me yake damunki"
tace "haka kawai hankalina bai kwanta da ita ba, ko dai zaka dawo wajenmu ka fara aiki?"
yayi dariya sosai yace "ban taɓa sanin ke matsoraciya bace sai yau"
tace "ba zaka gane ba idanunta sun nuna...."
yace "ga wannan"
kallo tayi taga chocolate ya mika mata, karɓa tayi zatayi magana cikin damuwa
yace "shiru kici"
shiru tayi ta ɓare saida ta cinye yace "kin san na waye?"
girgiza kai tayi
yace "na boss ɗina ce na sace miki"
waro ido tayi tace "kai idan ta sani fa?"
yace "saina ce kece na baiwa"
kamar zatayi kuka tace "ni dai wallahi tana bani tsoro"
har suka isa school nasu fahad yana kwantar mata da hankali kada taji tsoron manal babu komai da haka dai harya ɗauko fahad da Imran suna zaune a baya Imran yace "Ameesha kina lafiya kuwa?"
a hankali tace "ina lafiya Imran"
man yace "bata lafiya"
labarin abinda ya faru ya bashi daga karshe yace "ashe matsoraciya ce"
dariya suka kwashe dashi harda Imran, shiru tayi Imran ganin haka yace "to yaya ko dai zaka bar aikin ne kawai dan naga kamar hankalinta ba'a kwance ba"
yace "no inada tabbacin wannan aikin shine zai gyara rayuwarmu"
a ranta tace "Allah yasa kada ya wargaza rayuwarmu"
da kyar ta sake suka fara hira harma ta manta da damuwa tana bawa Imran hanu su tafa da haka har suka isa gida.
bayan ta koma gida suka kirata atake ta karɓi contract ɗin dan tasan zai kawo mata opportunity dayawa, cikin jin daɗi ta kwanta akan kafar ammi wacce ta rame ta zama shiru shiru tace "ammi kin san me?"
girgiza kai tayi tace "a,a manal"
tace "yau na samu na cika burins na haɗa hannu da manya manyan masu zane na duniya"
Ammi tace "wow congratulations manal Allah yasa kin fara a sa'a, a kullum ina miki addu'a duk abinda kika nema a duniya Allah ya baki"
rungume ƙafan ammi tayi tace "thank you ammi I love you"
s hankali tace "i love you too, gyara na gyara miki gashinki kina bari haka zai ɓaci dashi ke ma gashinki baya fishi"
gyara kwanciya tayi ammi tana gyara mata gashin ta kitse mata kitso biyu me kyau tace "yawwa yanzu kika zama manal"
murmushi tayi ta tashi daga kwancen ta rungumeta tareda ɗaura kafafunta a jikinta tayi shiru, ammi tace "manal?"
tace "na'am"
cikin sanyin murya tace "yanzu banida wani buri kamar naga kikyi aure, kin haifamin jikoki wanda zanyi wasa dasu"
murmushi tayi saide taji gabanta ya faɗi a ranta tace "aure kuma? to nida ko saurayi bana dashi?"
a fili tace "ammi na"
ɓoye fuskanta tayi a jikinta, murmushi ammi tayi, a hankali take tunano rayuwarta cikin ranta tace "inada saurayi kuwa? shin akwai wanda ya taɓa buɗe baki yace ina sonki manal?"
runtse ido tayi zuciyanta yana harbawa da sauri tace "babu, tun ina yarinya hanan sadik yana sonta ni kuma babu wanda yake sona a class namu, harna gama secondary babu wanda ya taɓa cewa manal ina sonki"
fara janye jikinta tayi daga na ammi ta zubawa ammi ido, ammi tace "menene?"
tashi tayi tana juyawa a hankali saida ta gama juyi idanunta suka koma jajur, ammi a tsorace tace "menene manal?"
hanun ammi ta damke cikin nata, cikin azaba ammi ta cije baki, bakinta yana rawa tace "ammi akwai wanda ya taɓa cewa yana sona?"
shiru ammi tayi dan babu, tace "akwai?"
shiru ta kuma yi, a mugun tsawace kamar zata fasa gidan tace "akwaiii?"
ammi ta girgiza kai tace "babu"
zama tayi a kasa ta ɗaura kanta a cinyar ammin wani irin kuka ta fashe dashi, Ammi tana shafa bayanta tace "me kikeyi haka manal?"
cikin kuka tace "meyasa ba'a sona? ko mata basa sona babu me zuwa wajena tun a school tun ina yarinya"
ɗago kai tayi hawayen ya wanke mata fuska ta share da sauri ta fara dariya, ammi ta gama tsorata da ita, tace "ammi kukan me nake? sabida ba'a sona? amma ai inada kuɗin da zaisa a soni ko?"
jijjiga kai ammi tayi, ta kamo hanunta tana dariya haɗe da hawaye tace "zan iya siyan soyayya koda a hannun waye ne ko ammi?"
jijjiga kai ammi tayi cikin son kwantar mata da hankali, tace "karna damu ko? na kwantar da hankalina ko?"
ammi tace "eh"
kwantar da kanta tayi a hankali ta fara bacci, busashen hawaye akan fuskanta.
*Jiddah Ce....*
08144818849
managarciya